Da Dumi Dumi

Ado Gwanja na cikin wasa a Legas aka shaida masa matarsa ta haihu

Ado Gwanja yana cashewa da yaransa
Ado Gwanja yana cashewa da yaransa

A ranar Lahadin da ta gabata ce shahararren mawakin nan dan wasan Hausa, Ado Gwanja ya yi Wasan Sallah a Legas a harabar gidan Rediyon Bond FM da ke daura da Oshodi. Wasan wanda ya kayatar sosai ya samu halartar mata da matasa wadanda suka yi fito daga sassan Jihar Legas domin kashe kwarkwatar idonsu. Sai dai mawakin yana cikin wasa ya samu labarin matarsa ta haihu lafiya a can Kano.

Daya daga cikin fitattun mawakan zamani na ’yan Arewa mazauna Jihar Legas Abudullahi Isma’il wanda aka fi sani da B Meri Aboki ko kuma dan Arewan Legas shi ne ya shirya taron ya kuma gayyaci Ado Gwanja tare da sauran mawakan da suka debe wa jama’a kewa ciki har da Tauraruwar Hamada wacce mawakiya ce ’yar Arewa da ke zaune a Legas.

A zantawarsa da Aminiya, B Meri Aboki ya ce sun shirya taron ne a lokacin Sallah domin su debe wa jama’a kewa domin a baya can ba a shirya irin wannan taron ’yan Arewa mazauna Legas ba su da wurin zuwa don shakatawa a lokacin Sallah da ya wuce bakin teku inda a lokuta da dama ruwan tekun kan tafi da yara idan sun je kallo suka shiga ciki. “Kuma mu da muke Agege tekun ya yi nisa da mu idan yara suka tafi iyayensu kan shiga fargaba don haka muka yanke shawarar shirya wannan taro domin debe musu kewa tare da bunkasa al’adunmu na Arewa. Don haka muke dauko mawaka daga Arewa domin su zo su taya mu murnar Sallah,” inji shi

Da yawa daga cikin mahalarta taron da Aminiya ta zanta da su, sun nuna farin cikinsu, inda suka ce ba su taba ganin Ado Gwanja ba sai a talbijin ko wayar salula amma yanzu sun gan shi ido-da-ido ya yi wasan da ya burge su

Haka zalika Sarauniyar Legas, Hajiya A’isha Shamaki wacce take cikin manyan bakin da suka halarta ta yi kira ga mata da matasa su dogara da kansu, ta ce shirye-shiryen nishadi da suka hada da rawa da waka ko wasan barkwanci ko na kwaikwayo hanyoyi ne da matasa da dama suka rike a matsayin sana’a don haka su ma matasan Legas kada su yarda a bar su a baya.

ADVERTISEMENT
 Ado Gwanja yana cashewa da Hausawan Legas
Ado Gwanja yana cashewa da Hausawan Legas

Wakilin Aminiya ya zanta da Ado Gwanja a ranar da ya gwangwaje ’yan Arewa mazauna Legas inda ya ce yana cike a ciki da farin ciki bisa kyautar da Allah Ya ba shi a ranar. Ya ce “ Ina tsakiyar wasa aka kira ni ta wayar salula aka shaida min Allah Ya sauki mai dakina lafiya, wannan ita ce haihuwata, ta farko. Kuma ina cike da farin ciki da jin dadin irin salon girmamawa da so da kauna da jama’ar Legas suka nuna min,” inji shi

Wadanda suka shirya taron sun sha alwashin ci gaba da gayyato fitattun mawakan Hausa daga Arewa domin nishadantar da al’ummar Arewa mazauna Legas.

Share