Da Dumi Dumi

AFCON 1984:  An yi wa Najeriya magudi – Onigbinde

Adegboye Onigbinde
Adegboye Onigbinde

Tsohon Kocin Super Eagles, Adegboye Onigbinde ya fasa kwai a wata hira da ya yi da tashar Cool FM da ke Abuja a shekaranjiya Laraba, inda ya ce an yi wa Super Eagles magudi a Gasar Cin Kofin Afirka da aka yi a 1984 lokacin da Eagles ta buga wasan karshe da Kamaru.

Kamaru ce ta lallasa Najeriya a wasan da ci 3-1 wanda ya gudana Abidjan da ke kasar Kwaddebuwa.

Onigbinde ya ce abin da ya daure masa kai shi ne yadda aka hada kai da wadansu jiga-jigai daga Najeriya don ganin kasar nan ba ta lashe kofin ba ko ta halin kaka a wancan lokaci.

Da aka tambaye shi ko me ya sa suka yi haka? Sai ya amsa da cewa Allah Shi ne Masani.

“Akwai shakku game da yadda aka yi alkalancin wasan, hakan ya sa aka doke Najeriya da ci 3-1. Bayan na yi bincike sai na gano akwai sa hannun wadansu ’yan Najeriya don ganin Super Eagles ba ta lashe kofin a wancan lokaci ba saboda son zuciyarsu,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Onigbinde ya taba buga wa kungiyar Super Eagles kwallo kafin ya zama kocinta. Yanzu haka yana da shekara 81 kuma ya koka game da yadda Hukumar NFF ta yi biris da shi a halin yanzu duk da irin gudunmawar da ya ba Najeriya a harkar kwallon kafa.

Jama’a sun yi mamakin ganin tsohon kocin bai fasa kwai ba sai bayan shekara 35 da faruwar lamarin.  Wannan ya sa wadansu ke tababa a game da ikirarinsa inda wadansu ke danganta shi da tsufar da ya yi.

Share