✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2019:  An bayyana kyaututtukan da Aljeriya da Senegal da Najeriya suka samu

A ranar Talatar da ta wuce ce Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) ta bayyana kyaututtukan da kasar Aljeriya wacce ta lashe kofin da…

A ranar Talatar da ta wuce ce Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) ta bayyana kyaututtukan da kasar Aljeriya wacce ta lashe kofin da Senegal da ta zama ta biyu da kuma Najeriya da ta zama ta uku suka samu.

A ranar Juma’ar da ta wuce ce aka kammala gasar kuma Aljeriya ce ta lashe kofin a karo na biyu bayan ta lallasa Senegal da ci daya mai ban haushi.

Kamar yadda rahotonni suka nuna, Aljeriya da ta lashe kofin ta samu kyautar Dala miliyan 4 da rabi ne (kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 624 da dubu 500) yayin da Senegal ta samu kyautar Dala miliyan 2 da rabi (kimanin Naira miliyan 902 da dubu 500).

Najeriya wadda ta kasance ta uku kuma ta samu lambar Tagulla ta samu kyautar Dala miliyan 2 ne (kimanin Naira miliyan 722).