A ci gaba da fafatawa a gasar neman hayewa gasar cin Kofin Afirka da zai gudana a Kamaru a badi, gobe Asabar ne ’yan wasan Super Eagles na Najeriya za su fafata da takwarorinsu na Libya a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo na Jihar Akwa Ibom.
Wannan shi ne wasa na uku, tun bayan da aka fara gasar.
A wasan da Najeriya ta yi na farko Afirka ta Kudu ce ta bi Najeriya har gida kuma ta lallasa ta da ci 2-0. A wasa na biyu ne Najeriya ta bi Seychelles har gida ta lallasa ta da ci 3-0 sai kuma gobe da Najeriya za ta hadu da Libya a wasa na uku.
Wasan na gobe zai gudana ne da misalin karfe 4 da rabi na yamma agogon Najeriya a filin wasa na Uyo.
Kawo yanzu Libya ce take saman teburi a Rukunin E da maki 4 sai Afirka ta Kudu ta biyu da maki 4 sai Najeriya a matsayi ta uku da maki 3, sai Seychelles ta hudu wadda ba ta da maki ko daya.
Idan Najeriya ta doke Libiya za ta hada maki 6 ke nan yayin da idan Libya ce ta samu nasara a kan Najeriya za ta hada maki 7.
Masana harkar kwallon kafa suna ganin wasan zai yi zafi ganin duk kasar da ta sake aka doke ta a wannan wasa, to za ta iya fuskantar matsala.
Rabon da Najeriya ta halarci gasar cin Kofin Afirka tun a shekarar 2013, kuma shekarar ce ta lashe kofin a karkashin horarwar marigayi Stephen Keshi. Ana gudanar da gasar ce duk bayan shekara 2.
Tun farko Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta bayyana cewa za a yi wannan wasa ne a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna amma daga baya ta canja shawara inda ta mayar da wasan zuwa filin wasa na garin Uyo a Jihar Akwa Ibom saboda wasu dalilai da suka hada da rashin kyan filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna.
Sannan a ranar Talata mai zuwa 16 ne Najeriya za ta bi Libya gida don su yi wasa zagaye na biyu.
Don haka wadannan wasanni biyu da za a yi gobe da kuma ranar Talata mai zuwa za su yi tasiri a kasashen biyu.
Duk kasar da ta zama zakara a kowane rukuni ne za ta haye gasar cin Kofin Afirka da zai gudana a Kamaru a shekara mai zuwa idan Allah Ya kai mu.