Da Dumi Dumi

AFCON 2019:  Kamaru ta fara yunkurin korar kocinta

Ministan Harkokin Wasanni na kasar Kamaru, Mista Narcisse Mouelle Kombi ya bayar da umarni ga Hukumar Kwallon Kafa ta kasar ta kori kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Clarence Seedorf.

Ministan ya ce hakan ya zama dole ganin kocin ya kasa tabuka abin-a-zo-a-gani a Gasar Cin Kofin Afirka da za a kammala yau a Masar.

Kamaru mai rike da kofin, an fitar da ita ce a zagaye na biyu bayan Najeriya ta lallasata da ci 3-2.

Haka kuma ganin yadda kungiyar Indomitable Lions ta Kamaru ta rika yin tangal-tangal tun a zagayen farkon ya sa akwai bukatar a sallami kocin a wannan lokaci. “Ku sanar da kocin irin yarjejeniyar da muka kulla da shi kafin ya zama kocin kungiyar.  Ko kusa bai cika alkawarin da ya dauka na yin abin kirki a Gasar Cin             Kofin Afirka ba, don haka akwai bukatar ku sallame shi a wannan lokaci,” inji Ministan a sakon da ya aike wa hukumar a ranar Talatar da ta wuce.

Idan Kamaru ta sallami Seedorf zai shiga sahun masu horarwar da aka sallama a gasar ta bana.

ADVERTISEMENT

Tuni Tanzaniya ta sallami kocinta dan asalin Najeriya Emmanuel Amuneke jim kadan bayan an fitar da kasar a gasar.

Kamaru ce ta biyu wajen yawan lashe kofin Afirka. Ta lashe sau biyar, sai Masar ce ta farko bayan ta lashe bakwai.

Share