Da Dumi Dumi

AFCON 2019: Najeriya ta zama ta uku

A shekaranjiya Laraba ne kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta zama ta uku a Gasar Cin Kofin Afirka da ke gudana a Masar bayan ta lallasa Tunisiya da ci 1-0.

Odion Ighalo ne ya zura kwallo daya tilo a raga tun a minti na uku da fara wasa da hakan ya sa Najeriya ta kasance a matsayi na uku a jerin kungiyoyi 24 da suka fafata a gasar ta bana.

A yau Juma’a ne ake sa ran za a samu kungiyar da za ta zama zakara da kuma wadda za ta kasance ta biyu a gasar a tsakanin Senegal da Aljeriya.

Sai dai Ighalo wanda kawo yanzu ya fi kowane dan kwallo yawan zura kwallaye a raga a gasar bayan ya zura kwallaye biyar, ya ji rauni a kokon gwiwarsa ta hagu a daidai minti na 44 da hakan ta sa aka canja shi.

Ighalo ya zama na biyu a ’yan kwallon Najeriya da suka taba zura kwallaye biyar  a raga a gasar cin kofin Afirka.  Na farko shi ne marigayi Rashidi Yekini.

ADVERTISEMENT

Odion Ighalo dan shekara 30, yana kwallo ne a kulob din Shengai Shenhua da ke kasar Sin.

Share