Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

AFCON 2019:  Nigeriya ta kai matakin Semi Fainal

A shekaranjiya Laraba ce kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta lallasa Afirka ta Kudu da ci 2-1 a wasan Kwata-Fainal a gasar cin Kofin Afirka da ke gudana a Masar.

Kwallaye biyun da ’yan kwallon Najeriya Chukweuze da Ekong suka zura a ragar Afirka ta Kudu ne suka ba Najeriya damar hayewa matakin kusa-da-na karshe wato Semi Fainal.

ADVERTISEMENT

A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu ne za a gudanar da wasannin kusa da na karshen.

Jim kadan bayan an kammala wasan na shekaranjiya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon taya murna ga kungiyar inda ya nuna farin cikinsa game da namijin kokarin da ta nuna wajen doke Afirka ta Kudu a wasan. Shugaban ya nemi su ci gaba da nuna kwazo a sauran wasannin da suka rage don ganin sun samu nasarar lashe kofin.

ADVERTISEMENT

Ya ce daukacin ’yan Najeriya sun zuba ido su ga yadda kungiyar za ta lashe kofin a wannan karo musamman ganin yadda muke tinkaho da zaratan ’yan kwallo.