Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

AFCON 2019:  Otedola ya cika alkawarin Dala dubu 25 da ya yi wa Super Eagles

femi-otedola

Fitacccen dan kasuwar nan Mista Femi Otedola a ranar Talatar da ta wuce ya cika alkawarin da ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles na ba su kyautar Dala dubu 25 (kimanin Naira miliyan 9 da dubu 50).

A yayin gasar cin Kofin Afirka da aka yi a Masar jim kadan bayan Najeriya ta lallasa Afirka ta Kudu a wasan Kwata-Fainal ne, Otedola ya yi alkawarin ba ’yan kwallon Super Eagles kyautar Dala dubu 25 a kowace kwallo da suka zura a raga a sauran wasanni biyu da suka rage musu.

ADVERTISEMENT

Sai dai Aljeriya ta lallasa Najeriya a wasan kusa da na karshe abin da ya sa Najeriya ta doke Tunisiya da ci daya mai ban haushi ta kasance ta uku.

Shi ma Attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin ba kungiyar kyautar Dala dubu 50 (kimanin Naira miliyan 18 da dubu 100) a kan kowace kwallo da suka zura a raga a wasan Semi Fainal har zuwa wasan karshe.

ADVERTISEMENT

Sai dai rahotanni sun ce har zuwa hada wannan labari Dangote bai cika nasa alkawarin ba.

Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) ta tabbatar da labarin cika alkawarin da Otedola ya yi  a shafin sadawarta na Twitter a ranar Talatar da ta wuce.

Odion Ighalo ne ya zura kwallo a ragar Tunisiya wanda hakan ya sa Najeriya ta kasance ta uku a gasar.