✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2019: Ranar 9 ga Janairu za a sanar da sabuwar kasar da za ta dauki nauyin gasar

Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) ta ce a ranar 9 ga watan Janairun 2019 ne za ta sanar da sabuwar kasar da za…

Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) ta ce a ranar 9 ga watan Janairun 2019 ne za ta sanar da sabuwar kasar da za ta dauki nauyin gasar kwallon Afirka ta bana.

A kwanakin baya ne Hukumar CAF ta kwace daukar nauyin gasar daga kasar Kamaru bayan ta kafa kwamitin bincike da ya tabbatar Kamaru ba ta shirya daukar nauyin gasar ba, inda kawo yanzu akwai filayen wasanni da otel-otel da sauran abubuwan da za a bukata a yayin gasar da Kamaru ba ta kammala ba. Kan haka ne hukumar ta kwace gasar daga Kamaru inda yanzu haka ta sake ba duk kasar da take sha’awar daukar nauyin gasar da ta gabatar da bukatar haka kafin ko ranar 14 ga Disamban nan da muke ciki.

Kawo yanzu dai kasashe biyu ne suka nuna sha’awarsu ta daukar nauyin gasar da ake sa ran farawa a watan Yunin badi. Kasashen sun hada da Maroko da kuma Congo-Brazzabille sai Afirka ta Kudu wadda  zuwa ranar Talatar da ta wuce ba ta yanke shawarar ko za ta shiga sahun masu sha’awar neman daukar nauyin gasar a wannan karo ba.

Wannan shi ne karo na farko da kasashe 24 za su fafata a gasar maimakon 16. Sannan shi ne karo na farko da za a gudanar da gasar a watan Yuni maimakon watan Janairu.

Kamaru ta nuna rashin jin dadi game da kwace gasar daga wurinta inda ta nuna akwai siyasa a cikin lamarin.