Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

AFCON 2019: Tanzaniya ta kori Amuneke

Hukumar Kwallon Kafa ta Tanzaniya (TFF) ta bayar da sanarwar korar kocinta dan asalin Najeriya, Emmanuel Amuneke.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafin sadarwarta na Twitter a ranar Litinin da ta wuce, ta ce ta kori kocin ne saboda rashin yin abin kirki a gasar cin Kofin Afirka da ke gudana a Masar.

ADVERTISEMENT

Tanzaniya wacce ta fafata a Rukunin C da kasashen Senegal da Aljeriya da Kenya an fitar da ita ce tun a zagayen farko bayan ta kasa samun ko da maki daya.

A wasanta na farko Senegal ce ta lallasa ta da ci 2-0 sai Kenya ta doke ta da  ci 3-2 yayin da Aljeriya kuma ta yi mata luguden kwallaye 3-0.

ADVERTISEMENT

Wannan dalili ne ya sa hukumar ta yanke shawarar raba-gari da Koci Amuneke.

Sai dai tarihi ya nuna Ameneke ne ya kai Tanzaniya gasar cin Kofin Afirka bayan kasar ta shafe shekarda 39 ba ta halarci gasar ba.