✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Agwan Atyap ya bukaci manoma da makiyaya su rika kai hankali nesa

Agwan Atyap (Sarkin Kataf) Mista Dominic Gambo Yahaya ya bukaci manoma da makiyaya su rika kai hankali nesa tare da kokarin sulhunta kansu cikin girmamawa…

Agwan Atyap (Sarkin Kataf) Mista Dominic Gambo Yahaya ya bukaci manoma da makiyaya su rika kai hankali nesa tare da kokarin sulhunta kansu cikin girmamawa idan wani ya shiga hakkin wani domin dukkaninsu abokan tafiyar juna ne.

Agwatyap Dominic Gambo Yahaya ya yi wannan kira ne a fadarsa da ke garin Zango a Karamar Hukumar Zangon Kataf jim kadan bayan kammala nadin dagatai biyu da wadansu Ardon Fulani  biyu.

Da ya waiwaya kan wadanda aka yi wa nadin, Mista Dominic Gambo ya jawo hankalinsu kan nauyin da aka dora musu, inda ya yi kira gare su da su yi kokarin kwatanta adalci a tsakanin jama’arsu musamman, manoma da makiyaya ta hanyar sulhunta tsakaninsu idan wata baraka na neman barkewa kafin ta ruru ta fi karfinsu. Ya ce yin gaskiya ne kadai, zai janyo musu biyayya daga wajen talakawansu.

“Idan kuma ya gagare ku sai ku yi maza ku kai maganar ga na gaba da ku. Sannan ku kasance jakadu nagari ga masarautarmu a duk inda kuke,” inji shi.

Da ya juya kan sauran mahalarta taron, Sarkin ya yi kira gare su da su yi kokari su fito manyansu da yaransu a yayin gudanar da kidaya ta kasa da ake shirin farawa nan gaba.

Wadanda aka nada sun hada da Usman Kajang; Dagacin Awak da Linus Mutuwa; Dagacin Fada Tsoho sai Alhaji Habu Abdullahi Ango; Ardon Machong da Alhaji Ibrahim Alhassan Babuga a matsayin Ardon Fulanin Kaceccere.

Da yake jawabi a madadin wadanda aka nada, Dagacin Machong, Linus Mutuwa ya mika godiyarsa ga Masarautar Atyap da suka zabo su don maye gurabun wadanda aka rasa, inda ya yi alkawarin shi da takwarorinsa za su kwatanta adalci. Sannan ya roki jama’arsu da su mara musu baya don samun nasara a mulkinsu.

Da yake yi wa Aminiya karin haske wajen shagulgulan bikin da aka gabatar bayan kowa ya koma yankinsa, Ardon Kaceccere Alhaji Ibrahim Alhassan Bagudu ya ce su ne zuriyar Kaceccere wanda ya zauna a wurin daruruwan shekaru inda ya ce akasarin Fulanin Kudancin Kaduna da na wasu sassa ana yi musu lakabi da Kaceccere idan sun fito daga zuriyarsa.

“Nan ne tushenmu tun iyaye da kakanni kuma wannan sarauta na gaje ta ce daga iyaye da kakanni. A da can mun samu labari ana nada Ardon Kaceccere ne daga Masarautar Zazzau kafin kirikiro Masarautar Zango a ci gaba da yi mana nadi a nan,” inji shi.

Ya ce “Chindo dan Yamusa da kake jin labari wanda ya kafa garin Keffi a Jihar Nasarawa daga zuriyar Kaceccere ya fito.”

Ya ce in ban da ’yan matsalolin da aka samu a shekarun baya suna zaune lafiya da sauran kabilu, inda ya yi kira ga mahukunta su rika hukunta duk wanda suka kama da laifin haddasa fitina, maimakon  sai an kama mutum daga baya a sako shi ya zo yana isgilanci.

Mai shekara 48, Ardo Alhassan yana da mata uku da ’ya’ya 17.