✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmadu Mu’azu zai koma APC

Jam’iyyar APC ta shirya tsaf don kabar tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu, kamar yadda wasu…

Jam’iyyar APC ta shirya tsaf don kabar tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu, kamar yadda wasu majiyoyi suka shida wa Aminiya.

Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa, Sanata Babayo Garba Gamawa da Alhaji Kaulaha Aliyu wanda babban aminin tsohon Gwamnan ne suka koma APC.

Ahmadu Mu’azu wanda ya fice daga kasar nan fiye da shekara uku ya dawo ne a watan Disamban bara, lokacin da ya aurar da ’yarsa. Mataimaki Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da manyan ’yan siyasar kasar nan da suka hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da dan takarar Shugaban Kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar duk sun halarci daurin auren a Bauchi.

Kuma tsohon Shugaban PDP din ya ziyarci fadar Shugaban Kasa a ranar 19 ga Disamban, inda ya gana da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo na tsawon awa biyu, sai dai ya ki ya amsa tambayoyin manema labarai  a lokacin game da manufar ziyarar.

Wannan ganawa da halartar daurin auren da Mataimakin Shugaba Kasa ya yi a Bauchi, ya sanya masu lura da al’amuran siyasa fara hasashen cewa tsohon Gwamnan na gab da komawa jam’iyyar a kowane lokaci.

To amma wata majiya a Jam’iyyar APC ta shaida wa Aminiya cewa shirye-shiryen karbar tsohon Gwamnan sun kankama a taron yakin neman zaben Shugaban Kasa na Shiyyar Arewa maso Gabas da za a yi a Bauchi da ake sa ran yi a gobe. Kafin haka Shugaban Kasa ya karbi wadansu manyan ’ya’yan PDP daga yankin na Arewa maso Gabas da suka sauya sheka zuwa APC ciki har da Tsohon Gwamnan Jihar Borno na Jamhuriya ta Biyu, Alhaji Mohammed Goni a ranar Litinin da ta gabata.

Da wakilinmu ya tuntubi Sakataren Tsare-tsare na APC a Jihar Bauchi, Lawan Gyan-gyan game da sauyin da aka samu, sai ya ce a halin yanzu APC ta kammala kakkabe PDP a jihar baki daya. Sannan ya ce game da dawowar Mu’azu APC ba abu ne da zai yi magana a yanzu ba, idan lamarin ya tabbata al’umma za su gani.