✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin lantarkin Katsina ya lashe Naira biliyan 4.5  ba ko kyalli

Kamar yau ne al’ummar kauyen Lambar Rimi da ke Karamar Hukumar Rimi a Jihar Katsina suka yi ta murna, shekaru 12 da suka gabata, lokacin…

Kamar yau ne al’ummar kauyen Lambar Rimi da ke Karamar Hukumar Rimi a Jihar Katsina suka yi ta murna, shekaru 12 da suka gabata, lokacin da aka kawo na’urori da kayan aiki ganga-ganga da nufin samar da wutar lantarki mai amfani da iska, mai karfin megawatt 10 a yankin nasu, aikin lantarkin da ake sa ran zai wadata birnin Katsina da kewayensa da wutar lantarki.

Kamar yadda Aminiya ta kalato, zuwa yanzu da aikin ya kai shekara 12 da farawa ya lashe zunzurutun kudi Naira bilyan hudu da miliyan 400, kuma murnar al’ummar yankin da na Jihar Katsina ta koma ciki. A wancan lokacin da aka tsiri aikin, an yi alkawarin kammala shi cikin shekara biyu, sai ga shi wankin hula ya kai dare, yau shekara 12 ke nan an kasa kammala shi.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci harabar da na’urorin suke shimfide a yankin a ’yan kwanakin nan, Malam Ahmad Aliyu da ke kauyen Bisau kuma yake makwabtaka da yankin ya bayyana cewa: “Mu dai tuni muka dawo daga rakiyar wannan aiki, domin kuwa an gaza ci gaba da aikin balle a kammala shi. A lokacin da aka fara aikin muna ta murna ganin cewa za mu rika samun wutar lantarki, sai ga shi an banzatar da aikin. Yanzu muna cikin bakin ciki da takaici, ganin cewa muradunmu na wutar lantarki ba za su tabbata ba, muna ci gaba da zama cikin duhu.”

Ya kara da cewa: “A lokacin da marigayi Gwamna Umaru ’Yar’aduwa ya kawo aikin a yankinmu, mun yi tsammanin za a kammala shi cikin kankanen lokaci, yadda kauyukanmu za su kasance cikin haske, amma yanzu muna ganin kila har abada ba za a gama aikin ba.”

Shi kuwa Sabi’u Muhammad a ganinsa, wannan aikin ya zama abin takaici da sanya damuwa ga mutanen kauyensu, musamman ganin yadda ake rufe hanyar da ke zuwa kauyen nasu a duk lokacin da aka tashi aiki daga harabar kamfanin aikin wutar lantarkin, domin kuwa wurin yana makwabtaka da su ne.

“Da zarar an ce maka yamma ta yi, ba za mu iya samun hanyar zuwa kauyenmu ba. Akan rufe hanyar da za ta sada mu da birni, don haka duk lokacin da aka samu wani mara lafiya ko mai wata lalurar da zai bukaci zuwa birni, dole sai dai a bi ta doguwar hanya. Don haka baya ga koken rashin kammala aikin nan, kuma muna fuskantar matsalar rufe mana hanya da ake yi,’ inji shi.

Da Aminiya ta ziyarci kauyen Lambar Rimi kuwa, ta gana da Bashir Mahmud, wanda ya ce babu shakka aikin samar da lantarkin yana tafiyar hawainiya, al’ummar kauyen suna ta korafin anya ma za su rayu su ga kammalar aikin! “A kullum muna ganin mutane daban-daban suna zuwa domin kallon aikin kuma suna komawa. Idan mun tambaye su sai dai su karfafa mana gwiwar cewa za a kammala shi nan ba da jimawa ba, to amma har zuwa yaushe za mu jira a gama aikin nan?” Shi a ganinsa, an yi asarar faffadan wuri, an daddasa turakun lantarkin da ba su da wani amfani.

“Tunda farko, ya kamata a ce Gwamnatin Tarayya ta bar mana filinmu mun ci gaba da nomawa, maimakon barinsa a haka yana lalacewa a banza,” inji Hamza, daya daga cikin mazauna kauyen na Lambar Rimi.

 

Sau shida ana saba alkawarin kammala aikin

Aikin samar da wutar lantarkin na Katsina mai aiki da iska da aka tsira shekara 12 da suka gabata, an yi ta daukar alkawarin kammala shi sau da dama amma ana sabawa. Tun a shekarar 2005 gwamnatocin baya suka yi ta sanya ranar kammala aikin da nufin kaddamar da shi, a lokacin marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa yana Gwamnan Jihar Katsina, inda daga bisani Gwamnatin Tarayya ta amshi aikin a shekarar 2007 daga hannun Gwamnatin Jihar Katsina. Gwamnatin Tarayya ta yi ta sanya ranar kammala aikin amma har yanzu shiru.

Tun farko, kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, Gwamnatin Tarayya ta mika wa wani kamfanin kasar Faransa mai suna Messrs Bergnet SA kwangilar aikin a shekarar 2010 a kan Fam miliyan 18 da rabi da alkawarin kammala shi cikin shekara biyu, wato a shekarar 2012 ke nan. Haka kuma a 2017, a cikin kasafin kudi na shekarar, Gwamnatin Tarayya a karkashin Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta kara ware Naira miliyan 904 da rabi domin kammala aikin. Sai dai kuma abin mamaki shi ne, daga wannan lokaci zuwa yau, an sanya alkawarin kammala aikin har sau shida, ba tare da an kammala ba.

Aikin samar da lantarkin ya gamu da matsaloli daban-daban, wadanda suka hada da lokacin da masu garkuwa da mutane don amsar kudin fansa suka yi garkuwa da wani injiniya dan kasar Faransa, Mista Collomp Francis da yadda aka yi ta lalatawa da sace wasu na’urorin samar da wutar da kuma yadda gwamnati ta yi ta banzatar da aikin wurin ta dalilin wasu ka’idoji na aikin gwamnati.

Aikin samar da wutar ya kunshi samar da manyan na’urori guda 37 da za su iya samar da wuta mai karfin kilowatt 275 tare da wasu na’urorin da za su iya murza iska, masu tsawon mita 55, wadanda kuma su ne za su tatso wutar daga iska. Ya zuwa yanzu dai an girka na’urori 16, a yayin da sauran suke yashe a kasa, wasu ma sun yi tsatsa, sun tasar wa lalacewa.

Wadansu masana harkar lantarki sun koka cewa, daga yadda aka bar na’urorin haka na tsawon lokaci, aikin yana iya zama na baban giwa. Sun ce kuma irin na’urorin da aka tanada domin aikin samar da megawatt 10, ba su da karfin da za su iya murza wadatacciyar iskar da za ta kai haka, domin kuwa karfin iskar da ke yankin ba wadatacciya ba ce.

Abdulkarim Muhammad El-Ladan, masanin al’amuran makamashi ne, wanda kuma ya yi nazari dangane da kimiyyar samar da wutar lantarki mai aiki da iska, ya bayyana wa Aminiya cewa abu ne mai wuyar gaske a ce wannan aiki zai yi tasiri, domin kuwa iskar da ke yankin ba ta da karfin da za ta murza na’urorin da aka samar.

Ya ce, “Karfin iskar da ke akwai a Katsina ba ta wuce gudun mita 3.5 a dakika daya ba kuma ana bukatar iska mai gudun mita 11 a dakika guda, wacce za ta iya murza na’urorin da za su samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 10. Wannan iska mai gudun mita 3.5 da ke akwai a Katsina ba za ta iya samar da kashi 20 cikin 100 na lantarkin da ake bukata ba, domin kuwa karfin iskar ya yi kadan matuka.” Ya ce wasu kasashe da suka ci gaba kamar Jamus, suna hada hikimomi fiye da daya domin samar da irin wannan lantarki. Suna amfani da ruwa da hasken rana da kuma bola wajen samar da lantarkin.

El-Ladan ya ce “Abin da irin wadannan kasashe suke yi shi ne, kasancewar karfin iska ba ta da tabbas, iska na zuwa kuma wani lokaci ta dauke, don haka sai su hada da ruwan teku, inda iska kan kada a duk tsawon shekara. Ta haka sai iskar ta hadu ta rika juya na’urar, wacce za ta samar da wutar.

“Ida ana son wannan tsari ya yi aiki a Katsina, ya zama wajibi a hada da ruwan dam, lokacin da iska ke da karfi sai a yi amfani da ita, idan kuma ta dauke sai a ci gaba da amfani da ruwa wajen murza na’urar da za ta ci gaba da samar da wutar,” inji shi.

Da yake bayyana tarihin wannan aiki na samar da wuta a Katsina, ya ce ’Yar’aduwa ne ya kirkiro aikin da nufin a rika amfani da shi wajen bincike da nazari ba wai domin ya samar da wutar lantarki ga al’ummar yankin ba. “Don haka wutar da na’urar za ta samar a lokacin hunturu ne kuma za ta wadata ne kawai domin bincike da nazarin kimiyya kamar yadda aka tsara, ba wai don ta ba gidajen mutane lantarki ba,” inji shi.

Wasu kungiyoyin ci gaban al’umma a Katsina sun yi ta yunkurin binciken yadda aikin yake, inda suka hada kwamiti domin haka. Shugaban wannan kwamiti, Bishir Ruwangodiya ya bayyana wa wakilinmu cewa kwamitin nasu ya ziyarci harabar da aka girke na’urorin har sau biyu domin ganawa da ’yan kwangilar aikin, wadanda suka bayyana musu cewa tsaikon aikin na wuyan Ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje.

“Rashin kammala aikin nan yana damunmu matuka kuma abin da ke kara ba mu mamaki shi ne yadda aka share shekaru masu yawa ba tare da an kammala shi ba. Muna roko ga Gwamnatin Tarayya ta cece mu, musamman idan aka yi la’akari da makudan kudin da aka kashe a aikin. Ya kamata a yi hanzarin kammala aikin nan domin al’ummar jiharmu ta amfana,” inji Ruwangodiya.

 

Wasu daga abubuwan da ke kawo wa aikin barazana

A cikin watan Fabrairu bara, jami’an Ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje sun yi rangadin duba aikin, inda suka tantance wasu daga cikin na’urorin da aka kafe. Wani jami’in tuntuba, wanda kuma shi ne Manajan Kamfanin O.T. Otis Engineering, Pius Onyenagubo ya taba bayyana cewa za a kaddamar da rabin aikin da aka kammala a cikin watan Maris na bara.

Ya ce a bara, “Na’urori 15 da aka kammala kafa su, za a kaddamar da su a karshen watan Maris, a yayin da sauran za a kaddamar da su a karshen shekara.” Ya kara da cewa 9 daga cikin 15 din ma an gwada su kuma sun yi aikin ba da lantarki mai karfin megawatt 4.5,  yayin da sauran 6 din suke bukatar gyara.

Haka kuma sun gano cewa 4 daga cikin na’urorin an lalata su, an sace wasu sassa na wayoyinsu.

Idan an kammala wannan aikin, za a iya hada wutar ta hanyar otel din Liyafa da ke Katsina, inda za a iya rarraba ta ga al’ummomin yankin. Daga lokacin da aka kara daga ranar kaddamarwar zuwa watan Oktoba, bara. Daga bisani dai sai aka sake saka ranar kaddamar da aikin zuwa watan Maris na bana, a lokacin da jami’ai daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya suka ziyarci wurin aikin lantarkin.

Ko a cikin watan Fabrairun bara, wakilinmu sai da ya ziyarci wurin aikin, lokacin da Daraktan da ke kula da al’amuran makamashi, Olatunbosun Owoeye ya bayyana batun biyan sauran kudin aikin da suka rage ga ’yan kwangilar, sannan ya samar da hanya zuwa wurin tare da nufin cewa za a kaddamar da aikin a bara.

Owoeye wanda shi ne ya wakilci Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa an samar da kudin kammala aikin na Katsina. Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, wanda mai taimaka masa na musamman ta fuskar samar da makamashi, Mansur Muhammad Musa, wanda shi ma injiniya ne, ya bayyana muhimmancin wannan aikin ga al’ummar jihar, domin kuwa zai bunkasa samar da wutar lantarki ga al’umma. Sai dai kuma duk da wannan yunkuri, har shekarar 2018 ta kare, ba a samu damar kaddamar da aikin ba.

A yayin da a kwanan nan wani kwamitin tantance aikin daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ziyarci yankin, injiniya mai kula da aikin, Emmanuel Yakubu ya ce na’urorin da ke aiki guda 16 ne kuma suna samar da lantarki mai karfin megawatt 4, a yayin da an kuma girka guda 21. Ya tabbatar wa wakilinmu cewa har yanzu al’ummar yankin ba su fara amfana da lantarkin ba.

Ya zuwa yanzu dai, kamfanin da ke kwangilar aikin, CREDCO Nigeria Limited ya dauki alwashin cewa zai mika kammalallen aikin a cikin tsakiyar Oktoban bana. Sai dai duk da haka, dan kwangilar ya koka da karancin wadatacciyar iska a yankin, inda ya ce an samu wadatacciyar iska ce a cikin watan Oktoban bara da kuma Fabrairun bana. Ya kara da cewa ana samun iska mai gudun mita 5 zuwa 12 a dakika daya a yankin.

Wannan bincike, Gidauniyar Daily Trust ce ta dauki nauyin samar da shi tare da tallafin Gidauniyar MacArthur.