✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin majalisa da aikin bangaren zartarwa duk daya ne –Sanata Shekarau

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Kano ta Tsakiya, Sanata Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano, ya cewa aikin majalisa da aikin bangaren zartarwa, duk daya ne.…

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Kano ta Tsakiya, Sanata Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano, ya cewa aikin majalisa da aikin bangaren zartarwa, duk daya ne.

Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, inda ya je don halartar dauren auren Shugaban Makarantar Koyar da Karatun Alkur’ani ta  Ibn Mas’ud da ke Ganganre Jos, Malam Kabiru Muhammad Chidawa. Sanata Shekarau ya ce majalisa ba ta fi bangaren zartarwa ba, haka bangaren zartarwa bai fi majalisa ba. Don haka babu wani dalilin rigima a tsakaninsu.

“Babu illa don bangaren zartarwa ya shawarci bangare majalisa wajen shirya kasafin kudi. Domin a karshe su ne ake kaiwa, su sanya hannu. Don haka idan bangaren zartarwa za su shirya kowace irin doka, ya kamata su shigo da ’yan majalisa su yi tare, idan aka yi haka ba za a sake jin wata rigima ba,” inji shi.

Sanata Ibrahim Shekaru ya ce don haka daya daga cikin aikin da zai sanya a gaba, shi ne zai yi duk abin da zai iya don ganin bangaren zartarwa da bangaren majalisa sun  fahimci cewa dole sai an hadu an tafi tare, sannan ’yan Najeriya za su ji dadi.

Daga nan ya yi  kira ga al’ummar Najeriya su rungumi juna su zauna lafiya. Ya ce zaman lafiya a tsakanin al’ummar Najeriya ne zai kawo hadin kai da ci gaba.

Ya ce idan babu zaman lafiya babu yadda za a iya samar da ayyukan yi a Najeriya. Domin masu zuba jari ba za su shigo kasar nan, su zuba jari ba.