✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan tafiyar wata biyu

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, a safiyar yau Lahadi ta dawo gida Najeriya bayan shafe wata biyu a kasar waje. Majiyarmu ta gano cewa uwarjgigdan…

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, a safiyar yau Lahadi ta dawo gida Najeriya bayan shafe wata biyu a kasar waje. Majiyarmu ta gano cewa uwarjgigdan shugaban ta fita daga Najeriya ne a watan Agusta zuwa kasar Saudiya don yin aikin hajji daga bisani ta wuce kasar Birtaniya.

Aisha Buhari ta sauka ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 4:30 na asuba.

Mai magana da yawun uwargidan shugaban Najeriya Suleiman Haruna, ya tabbatar da dawowar Aisha Buhari gida Najeriya.