✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aisha Buhari ta ja hankalin Iyaye Mata kan muhimmancin kula da lafiya

A matsayinki na uwa ga yara, kina da bukatar a baki shawarar yadda za ki kula da su.

Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, ta yi kira ga mata da su rika zuwa a na duba lafiyarsu akai-akai don guje wa kamu wa da cututtuka masu janyo mutuwar farad-daya kamar ciwon suga da hawan jini da cutar daji da sauransu.

Hajiya Aisha, ta yi wannan kira a ranar Talata a wani taron wayar da kai da aka gudanar a birnin Ilorin da ke jihar Kwara, inda ta tuna wa mahalarta taron muhimmancin lafiyarsu da ta ’ya’yansu.

Uwargidan Shugaban Kasar wadda ta samu wakilcin Daraktan yada labarai na ofishin Matar Shugaban kasa a wurin taron, Suleiman Haruna, ta jaddada muhimmancin da iyaye mata ke da shi wurin shayar da nonon uwa da bayar da zai samar da sunadarin gina jiki don inganta lafiyar yara.

Wata uwa da ta halarci taron

Ta ce, “a matsayinki na uwa ga yara kanana masu taso wa, kina da bukatar a baki shawarar yadda za ki kula da su da yadda za ki karfafe su da ba su kariya.”

Aminiya ta ruwaito an gudanar da wannan shirin ne a karkashin gidauniyar Aisha Buhari Foundation (ABF) da kungiyar Future Assured, wadda ta mayar da hankali a fanni lafiya da ilimi da sana’o’i da sauransu.

Gidauniyar Aisha Buhari (ABF), ta yi nasarori da dama a wadannan fannuka tare da hadin gwiwar jagorori da dama, musamman Uwargidan Gwamnan jihar Kwara wadda ita ma ta bayar da gudunmawa a bangarori da dama.

Wani sashe na iyaye mata da suka halarci taron

A nata jawabin a wurin taron, Mai dakin Gwamnan jihar Kwara, Dokta Olufolake Abdurrazak, ta tabo bangarori da dama, inda ta bukaci matan jihar Kwara da su bayar da na su goyon bayan a duk lokacin da aka bukaci haka, musamman a fannin kula da lafiyarsu.

Ta bukaci da su halarci taron makonni masu zuwa da za a gudanar a jihar a kan rigakafin cutar shan inna, tare da neman da su yi rijista da shirin da Gwamnatin da kaddamar a kwanan nan na tsarin inshorar lafiya.

Dokta Abdurrazak ya jinjinawa Uwargidan Shugaban Kasar kasancewarta a kan gaba wurin jajirce wa domin kula da lafiyar iyaye mata da yara, a yayin da ya yi daidai da kudurin Gwamnati na samar da cikakken tsarin kula da lafiya.

A wurin taron an raba kayayyakin karbar haihuwa da suka hada da kayan jarirai ga daruruwan iyaye mata da suka halarci taron.

Mai magana da yawun uwargidan shugaban kasa, Aliyu Abdullahi, a bayanin da ya gabatar ya bayyana ce wa, taron ya samu halartar Kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Raji Rasak da takwararsa ta al’amuran mata, Mrs Deborah Aremu da Babban Sakatare a Karamar Ma’aikatar Kula da Lafiya, Dokta Nusiat Alelu da Babban Darakta na Cibiyar Tallafa wa Al’umma ta Ajike People’s Support Center, Mr Abdulganiu Opeloyeru.