✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ajagun ya samu nasarar komawa kulob din Panathinaikos

A ranar Talatar da ta gabata ne Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) na Najeriya Abduljaleel Ajagun ya sanya…

Abduljaleel AjagunA ranar Talatar da ta gabata ne Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) na Najeriya Abduljaleel Ajagun ya sanya hannu a kwantaragin shekara hudu a kulob cin Panathinaikos da ke Girka bayan an kwashe lokaci mai tsawo ana takaddama a tsakaninsa da kulob din.
Don haka nasarar sanya hannun da dan kwallon ya yi za ta sa tsohon kulob dinsa na gida watau Dolphins zai samu kason Yuro dubu 200 kwatankwacin Naira miliyan 43.
Kulob din Panathinakos dai ya yi alkawarin biyan Dolphins kudin kafin karshen makon gobe.
Majiya mai karfi ta shaidawa kafar sadarwa ta MTNFootball.com cewa tuni Ajagun ya bar kasar nan zuwa Girka don cigaba da yin wasa a sabon kulob dinsa bayan an cimma yarjejeniya a tsakanin kulob din da na Dolphins.
Rahotanni sun nuna Ajagun har ya fara fitar da rai bayan da kulob din ya fara nuna masa wadansu halaye a can Girka a kwanakin baya da suka neme shi a matsayin gwaji amma bayan an sanya shi a wani wasa na tsawon minti 40 kacal ta sa kulob din yanke shawarar ya saye shi.
Idan za a iya tunawa, Ajagun shi ne kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) a gasar cin kofin duniya na matasa da ya gudana a Turkiyya a kwanakin baya.
dan kwallon ya samu nasarar jefa kwallaye uku a raga a yayin gasar kafin kasar Uruguay ta fitar da su a matakin zagaye na biyu a gasar.
kasashen Turai da dama da suka hada da Turkiyya da Kuroshiya (Croatia) sun nuna sha’awarsu a kan dan kwallon amma ya gwammace ya tafi Girka don cigaba da buga kwallonsa a can.