✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ajimobi na nan da ransa, inji iyalai

Iyalan tsohon Gwamnan jihar Oyo Sanata Abiola Ajimbo sun tabbatar da cewa yana nan da ransa. Hakan na zuwa ne sakamakon fargabar da jita-jitar rasuwar…

Iyalan tsohon Gwamnan jihar Oyo Sanata Abiola Ajimbo sun tabbatar da cewa yana nan da ransa.

Hakan na zuwa ne sakamakon fargabar da jita-jitar rasuwar jigon a jam’iyyar APC ta haifar da kuma kiraye-kiraye domin tabbatar da gaskiyar halin da yake ciki.

Surukarsa kuma ‘yar gidan gwamnan jihar Kano Fatima Ganduje ta tabbatar a wani sako da ta wallafa cewa mahaifi na mijinta na nan da ransa.

“Mun gode da sakonninku, amma babanmu na nan da ransa, alhamdulillha. Idan lokaci ya yi tabbas kowa zai mutu, amma dai da sauran lokaci…,” ta wallafa a shafinta ta Twitter a daren Alhamis.

Kazalika mai magana da yawun Ajimobi, Bola Tunji ya karyata labarin rasuwan ubangidan nasa ta shafinsa na Facebook.

“Ku yi watsi da jita-jitar. Rade-radi ne. Muna dai kara yin addu’a,” inji shi.

Yanzu kimanin makonnin biyu ke nan da aka killace Ajimobi sakamakon kamuwarsa da cutar coronavirus.

Shi ne wanda Kwamitin Amintattun jam’iyyar APC ta ayyana a matsayin shugaban jam’iyyar na riko bayan dakatar da Shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole a ranar Laraba.