Da Dumi Dumi

Akalla jirgi 18 suka sauka a Sakkawato a bikin ’yar Sarkin Musulmi

Wadansu daga cikin manyan baqi a wajen daurin auren ’yar Sarkin Musulmi a Sakkwato
Wadansu daga cikin manyan baqi a wajen daurin auren ’yar Sarkin Musulmi a Sakkwato

Aranar Asabar ce Sakkwato Birnin Shehu ya cika makil da manyan mutane daga ciki da wajen Najeriya, inda suka taru domin yi wa Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar kara don halartar bikin auren ’yarsa.

Wata majiyar ta labarta wa Aminiya cewa kusan Naira miliyan 200 Gwamnatin Jihar  Sakkwato ta ware domin bikin saboda gyara garin tare da kawar da datti a ko’ina, kuma duk wanda ya zo kada ya yi korafin abinci ko abin sha ko abin hawa.

Akalla jirgin sama 18 ne suka sauka a Sakkwato tare da manyan mutane domin halartar daurin auren.

An yi daurin auren na ’yar Sarkin Musulmi mai suna Fatima Abubakar da angonta Mahmood Yuguda, dan tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuuda a Masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke Sakkwato bisa sadaki Naira dubu 50.

Manyan mutanen da suka halarci bikin sun hada da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Malam Abba Kyari wanda ya jagoranci ayarin wakilan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Sakataten Gwamnatin Tarayya  Mista Boss Mustapha da Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu da Ministan Albarkatun Ruwa Alhaji Suleiman Adamu.

ADVERTISEMENT

Haka kuma gwamnonin jihohin Kebbi Sanata Atiku Bagudu da Filato Simon Bako Lalon da Adamawa Ahmadu Fintiri da Zamfara Muhammad Bello Matawalle da Imo, Emeka Ihedioha da Neja Abubakar Sani Bello duk sun halarci daurin auren.

Haka sarakuna sai wanda aka gani domin kusan duk sarakunan Arewa sun halarta.

A bangaren malamai, Farfesa Shehu Galadanci da Sheikh Karibullah Nasiru Kabara da sauransu duk sun halartar daurin auren.

Share