✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akalla Mahajjata 313 ne suka bar shan taba sigari bayan aikin Hajjin bana

Akalla Mahajjata dari 313 daga kasashe duniya ne suka yi watsi da shan taba sigari bayan kamalla aikin Hajjin bana a kasar Saudiya.‎ Mahajjatan sun…

Akalla Mahajjata dari 313 daga kasashe duniya ne suka yi watsi da shan taba sigari bayan kamalla aikin Hajjin bana a kasar Saudiya.‎

Mahajjatan sun dauki matakin ne bayan sun ziyarci asibitin kafa‎ da ke a Mina, kamar yadda Jaridar kasar ta Arab News ta sanar.

Abdullah bin Dawwod Al-Fayez, shugaban asibitin kafa a Makkah ya bayyana cewa,‎ Mahajjatan suna zuwa karbar magani a asibitin ne a Mina a karkashin wani hadin gwiwa da Gidauniyar Abu Ghazaleh da Ma’aikatar Lafiya da Ma’aikatar Kula da Aikin Hajji da Umrah da Sashen yaki da shan sigari na ma’aikatar Lafiyar wanda kwamitin wayar da kai akan hatsarurrukan da ke tattare da shan taba sigari a garin Makka ke lura da shi da kuma ofishin masarautar kasar mai Kula da masallatan Makka da Madina.

“Sakamakon abin sha’awa ne a bana domin akalla Alhazai kusan dubu113,000 suka amfana da asibitin tafi da gidanka wanda ke wayarwa da mutane kai.

” Asibitin ya rabar da kasidai, da takardun asibiti ga misakai 11,480 a madadin taba sigari wanda aka ajiye domin wayarwa da jama’a kai. Wannan shi ne karo na hudu da ake gudanar da wannan shiri kuma yana wayarwa da mutane kai ne akan hatsarin shan taba sigari tare da basu damar yin watsi da taba sigari musamman a lokacin aikin hajji,” inji Al-Fayez.