✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akalla mutum 15 sun mutu a fadan kabilanci a Cross River

Kimanin mutum 15 ne suka rasa rayukansu a tsakiyar mako a karamar hukumar Biase ta jihar Kuros Riba sakamakon fadan kabilanci. Fadan ya barke ne…

Kimanin mutum 15 ne suka rasa rayukansu a tsakiyar mako a karamar hukumar Biase ta jihar Kuros Riba sakamakon fadan kabilanci.

Fadan ya barke ne a tsakanin al’ummar Afono da ta Ibini ranar Laraba bayan da matsan Afono suka tare hanya suka hana ’yan Ibini wucewa.

Ita dai wannan hanya da ta jawo takaddama da asarar rayuka it ace hanya daya tilo da ko wacce daga cikin kabilun biyu za ta bi zuwa kauyenta.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ’yansandan jihar Kuros Riba DSP Irene Ugbo game da lamarin, amma ta karyata mace-macen.

“Babu asarar rai ko daya a rikicin; an yi shi amma kura ta lafa bayan an tura jami’anmu,” inji ta.

Ta kara da cewa gonaki da gidaje kawai aka lalata.

Kabilun biyu dai sun shafe sama da shekara biyu suna fada da juna.