Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Akantan coci zai shekara 18 a kaso kan satar Naira miliyan 15

Akantan coci zai shekara 18 a kaso kan satar Naira miliyan 15

An yanke wa akantan wani coci daurin shekara 18 a gidan yari bisa laifin satar Naira milyan 15.5 na gidauniyar tallafi.  Akantan mai suna Ibrahim Aku na majami’ar Church of Brethren a Jihar Adamawa, ya amsa laifuffuka shida da aka tuhume shi da su  da suka hada da kwace da karbar kudi ta hanyar sojan-gona, kamar yadda jaridar Banguard ta ruwaito. Hakan ya sa kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara uku kan kowane laifi, inda zai shafe shekara uku ke nan.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) wadda ta shigar da karar, ta wallafa hoton mai laifin, wanda Babbar Kotun Jihar ta yanke wa hukuncin. Kotun ta saurari karar da ke cewa an bai wa akawun amanar kudin da cocin ke karba a matsayin na taimako. Masu shigar da kara sun yi zargin cewa Aku tare da wani mai taimaka masa wanda a yanzu ya shiga wasan buya, sun yi takardun banki na bogi; amma ba su sa kudin a ma’ajiyar bankin cocin ba. Bayanai sun cewa Aku ya tura wa mai taimaka masan Naira dubu 500 a matsayin ladansa.

Babbar Kotun ta umarci Aku ya dawo wa cocin da kudin kuma za a sayar da duk wani abu da ya saya da kudin don mika wa cocin.