✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Akwai albarka a kasuwancin rake’

Garin Burga da ke Gundumar Dull a Karamar Hukumar Tafawa Balewa da ke Jihar Bauchi,  gari ne mai nisan kilomita 22 daga garin Tafawa Balewa.…

Garin Burga da ke Gundumar Dull a Karamar Hukumar Tafawa Balewa da ke Jihar Bauchi,  gari ne mai nisan kilomita 22 daga garin Tafawa Balewa.

Mafiya yawan al’ummar yankin manoma ne da suka mai da noma da kasuwanci suka zame musu abin dogaro.

Matasan yankin sun fi maida hankali wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci, musamman sayar da rake wanda shi ne kasuwancin da suka ce ya fi riba.

A zantawa da suka yi da Aminiya wadansu matasan kauyen Burga, sun ce sun fi gane wa wannan kasuwanci na sayar da rake kuma yana da riba, inda suka ce suna samun abin da za su ci kuma su taimaka wa iyayensu

Wani matashi mai suna Mohammed Hassan da ke sayar da raken, ya ce ya fara wannan kasuwanci ne tun yana dan shekara 15 tare da mahaifinsa, kuma ta sayar da rake Allah  Yake rufa musu asiri suna ci suna sha suna yin sutura suna kuma biyan bukatun yau da kullum.

Mohammed ya ce daga cikin kudin da ya samu riba na sayar da rake yake biyan kudin makarantar sakandare da ke Bununu. Kuma ya ce yana fata da sayar da rake zai iya biya wa kansa kudin makaranta a kwaleji ko jami’a.

Ya ce a kowace rana yakan yi cinikin Naira 1,000 zuwa 1,500. A ranar da ba a samu kasuwa ba ne yake yin kasa da haka amma a kullum yakan yi fiye da Naira 500.

Sai ya shawarci matasa su farka daga barci su fara sana’a ko kasuwanci komai kankantarsu maimakon dogara ga iyayensu ko su rika bin ’yan siyasa. “In mutum ba ya kasuwanci ko wata sana’a ba wanda zai yi sha’awar ya rika taimakonsa, don mutane za su dauka ba ya da wani amfani, sai su dauka  shi mutum ne marar kima da bai san ciwon kansa ba. Don haka in kana so a yi da kai a rayuwa tilas ka kama kasuwanci ko sana’a ta yadda za ka samu abin da za ka dogara da shi maimakon bin kwararo kana yawon banza ko shan miyagun kwayoyi,” inji shi.

Mohammed Hassan wanda ya ce yana da ’yan uwa bakwai wadanda yake taimakonsu daga lokaci zuwa lokaci, ya ce ba ya da buri kamar ya yi karatu a jami’a in ya kammala ya shiga aikin soja.

Ya ce zai yi karatu sosai domin ya cika burinsa na shiga aikin kare rayuka da dukiyoyin jama’a don ba ya jin dadin yadda matsalar tsaro ke addabar kasar nan. Ya ce ya kamata jami’an tsaro su samu daukin shugabanni su rika yin fiye da abin da suke yi a yanzu. “A kullum matsalar tsaro na damuna kwarai da gaske,” inji shi.

Wani matashi mai suna Sagir Ibrahim wanda aka fi sani da Sagir Kwada, ya ce saboda matasansu sun kama sana’a da kasuwanci da wuya a gansu cikin masu aikata miyagun laifuffuka.

Ya ce matasa a Burga masu kwazo ne da kishin neman na kansu, kowa a cikinsu yana neman na kansa suna kasuwancin kayan lambu kamar albasa da tumatir da tattasai da attarugu ga kuma harka mai riba ta sayar da rake. Kuma suna noman rani da damina, shi ya sa ba sa cikin masu aikata miyagun laifuffuka.

Ibrahim ya ce suna rokon gwamnati ta taimaka musu, inda ya ce suna bukatar takin zamani da kayayyakin feshi da magungunan kwari, kuma suna rokon gwamnati ta ba su rance domin su bunkasa kasuwancinsu.

Ya ce a kowace rana suna samun riba kuma suna taimakon iyayensu da kannensu, saboda haka suke neman taimakon gwamnati don inganta sana’o’insu.

Wata mai sayar da abinci a garin Burga, Hajiya A’isha Mohammed, wacce aka fi sani da Maman Burga ta ce abin da suke bukata shi ne tallafi daga gwamnati ko masu bada agaji don bunkasa kasuwancinsu.

Ta ce, “Al’amura sun dan yi tsanani shi ya sa ba mu da kudin da za mu sayi abinci isasshe da za mu sayar ga jama’a  amma idan aka dan tallafa mana to al’ummarmu za su saya za a samu riba sosai.”

A’isha wacce take da ’ya’ya hudu, ta ce ta hanyar sayar da abinci take ci kuma take ciyar da ’ya’yanta tana biya musu dukkan bukatunsu na makaranta, yayin da ’ya’yan suke taimaka mata wajen wanke kwanuka da kananan aikace-aikace a gida.

Wani shugaban al’umma Alhaji Musa Talle, mai shekara 63, ya ce al’ummar Burga suna fama da matsaloli domin sai sun yi tafiya mai nisa kafin su samu damar kiran wayar hannu. Ya ce “Ina kira ga gwamnati ta taimaka mana domin ciyar da kasuwancinmu da sana’o’inmu gaba.”

Talle ya roki gwamnati ta samar musu da irin rake mai inganci da kayayyakin noma na zamani domin su samu damar bunkasa noma da kasuwancin da matasansu ke yi.