✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai alfanu a noman ciyawa – Dan Saude

Manajan Daraktan  Gidan Gonar Dan Saude Farm da ke garin Kwadom a Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Muhammad Dan Saude, ya…

Manajan Daraktan  Gidan Gonar Dan Saude Farm da ke garin Kwadom a Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Muhammad Dan Saude, ya bayyana alfanun da ke tattare da noman ciyawa.

Ahmed Dan Saude ya bayyana haka ne lokacin da Aminiya ta ziyarci gonar  don gane wa idonta yadda ake noman ciyawa don samar da abincin dabbobi.

Ya ce ya yanke shawarar fara noman ciyawar ce lokacin da ya fara kiwon shanun da ya sayo daga kasar waje. Ya ce da ya fuskanci matsalar abincinsu, sai hakan ya zaburar da shi wajen fara noman ciyawa don sauwake wa kansa matsalar abincin dabbobi.

Dan Saude ya ce wata daga cikin ciyawar ya sayo ta ce daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kuma Jihar Jigawa, wata kuma daga kasar waje.

Ya ce duk bayan kwana uku ake yanke ciyawar kuma idan aka yanke ta za ta sake tsirowa kamar ba a yanke ba, hakan ya sa yake yanke ta y daure gammo-gammo ana zuwa ana saya.

A cewar Ahmed Dan Saude a gonar akwai bangarori da yawa, ciki har da inda yake sarrafa ruwan leda kuma yana shirin fara sarrafa ruwan gora.

Ya ce gonar mai ma’aikata 250 tun kimanin shekara 12 da suka gabata ya bude ta inda ya fara da kiwon tsuntsayen salwa ya zo ya sa kaji 5,000 – inda suka kai 50,000.

Ya bukaci tallafin gwamnati wajen samar musu da injuna na musamman don yanke ciyawar ya nade ta.Ya ce ciyawar, akwai wacce take kara wa shanu ruwan nono da nama, kuma idan zabi suna ci yana sa su yin kwai a kai-a kai.