✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai bukatar gwamnati ta tallafa wa mawaka – Voice of G

Gideon Yakubu wanda aka fi sani da Voice of G, mawakin Hip-hop ne na Hausa da ke Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce yawancin…

Gideon Yakubu wanda aka fi sani da Voice of G, mawakin Hip-hop ne na Hausa da ke Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce yawancin mawaka suna da basira sai dai ba su da masu tallafa musu musamamn wajen yin albam, wanda hakan yakan sa gwiwarsu ta yi sanyi wajen ci gaba da abin da suke yi.  Ya kuma yi kira ga gwamnati ta tallafa musu don ganin harkar waka ta ci gaba:

 

Aminiya: Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?

Voice of G:  Sunana Gideon Yakubu. Amma an fi sani na da Voice of G. Ni mutumin Jihar Filato ne.  An haife ni a Jihar Kaduna kuma a can na yi karatun firamare, amma na yi karatun sakandare a mahaifata Jihar Filato. Bayan na fara waka sai na samu aiki a wani situdiyo inda ake buga wakoki. Bayan wannan ne na zo Kano na hadu da wani kamfani na Record Label, Black Gold Records, wadanda a yanzu haka suke ci gaba da taimakona.

 

Aminiya: Yaya aka yi ka fara waka?

Voice of G: Zan iya cewa na fara waka daga wakokin coci daga baya kuma sai abin ya canja na shiga yin wakokin Hip-hop. Sai dai yadda na fara wakar Hip-hop, ba abu ne mai sauki a gare ni ba, domin gaskiya na sha wuya sosai kafin na samu in iya. Zan iya tunawa na fara waka tun a shekarar 2007. A wancan lokaci idan mutun ya je situdiyon ma idan bai iya wakar ba sai a ce ya tafi ba zai yi ba. Amma haka muka ci gaba da yi har Allah Ya taimaka mana muka kawo matsayin da muke kai a yanzu, duk da cewar har yanzun koyo muke amma mun gode Allah.

 

Aminiya: Zuwa yanzu wakoki nawa ka fitar?

Voice of G: Wakokina za su kai tamanin da wani abu sai dai har yanzu ban yi albam ba. Amma a yanzu  akwai  wani albam da nake aiki a kansa tare da  wani mawaki K7  mai suna ‘Yarinyar Arewa’ kuma muna tsammanin zai fito a watan  nan na Janairu. Sannan akwai wani albam nawa wanda nake aiki a kansa mai suna ‘Better Pikin’. wanda nake sa rai zan fitar da shi nan ba da dadewa ba.

 

Aminiya: Wace kungiyar mawaka kake ?

Voice of G: Ina cikin kungiyar Black Gold Label babu abin da zan ce da wannan kungiya sai godiya domin tunda na zo na fara waka tare da su muke suna ba ni duk wata gudunmawar da nake bukata. A takaice ma zaman da nake yi da su ne ya sa na karu da samun gogewa a harkar waka.

 

Aminiya: Ana zargin mawaka da rashin hadin kai, a ganinka, me ke kawo haka?

Voice of G: To a nawa ganin wadansu ne ke bata wadansu, domin da na zo Black Gold Record ba haka na tarar ba. Sun nuna min so da kauna da kuma daraja kowa saboda haka, mu a nan muna hada kanmu.  Idan mutum ya yi waka ana haduwa a gyara masa tare da ba shi kwarin gwiwar da yake bukata. Yawancin abin da ke kawo rashin hadin kan bai wuce wani ya samu daukaka a rika yi masa hassada ba. Kuma wannan ba hali ne mai kyau ba. Daukaka ta Allah ce. Kamata ya yi kai ma ka dage ka rika yin aiki mai kyau wannan zai ja maka daukaka maimakon ka zauna kana yi wa wani hassada hakan babu inda zai kai mu sai ci baya.

 

Aminiya: Wane ne gwaninka a cikin sauran mawaka kuma wa kake koyi da shi?

Voice of G: Wizkid ne gwanina saboda ni ina koyi ne da irin salon wakokinsa.

 

Aminiya: Wane kira za ka yi ga sauran mawaka ?

oice of G:To abin  da  zan gaya musu shi ne cewa  harkar waka ba abar wasa ba ce saboda haka dole mutum ya jajirce wajen ganin harkar tana tafiya yadda ya kamata. Dole ne mutum ya kara da hakuri wajen mu’amala da mutane da kuma masoyanka. Kuma ya kamata a daina gaba da hassada saboda son kai, ba abu ne da zai ciyar da harkar waka gaba  ba.

 

Aminiya: Bayan wakokin Hip-Hop, shin kana wakokin nanaye ko wakar fim?

Voice of G: A’a, ba na yin kowane wakoki sai na hip-hop kawai wato irin su R&B ba rap ba.

 

Aminiya: Shin kana wakokin siyasa?

Voice of G: Shi ma wannan bangare ban taba yi ba sai dai na yi wakokin fadakarwa ga jama’a a kan sha’anin rayuwa da sauransu.

 

Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwammnati?

Voice of G: A cikin albam din da na yi wato ‘Better Pikin’, na yi kira ga gwammnati cewa ta taimaka wa harkar waka. Wadansu na da baiwar yin wakar amma ba su da mai tallafa musu.  A yawancin kasashen da suka ci gaba za ka tarar gwamnati tana taimaka wa mawaka yadda ya kamata, wanda yake sanyawa su tsaya da kafafunsu. Idan gwamnati ta duba za ta ga cewa idan wadannan mawakan suka tsaya da kafafunsu to ta rage nauyin mutane da za ta sama wa aikin yi. Kuma su kansu idan suka kafu za su dauki wadansu mutane aiki a karkashinsu hakan zai rage yawan marasa abin yi a cikin al’umma. A yanzu matasa da dama ba su da abin yi sun dogara ne kacokan kan iyayensu wanda kuma hakan bai dace ba. Saboda haka akwai bukatar gwammnati ta taimaka wa mutane musamman matasa wajen ganin sun samu abin yi.