✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai bukatar gwamnati ta tallafa wa mawaka – Hamisu Asaki

Hamisu Asaki yana daga cikin mawaka da ke tasowa a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa kananan mawaka suna fuskantar matsala ta…

Hamisu Asaki yana daga cikin mawaka da ke tasowa a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa kananan mawaka suna fuskantar matsala ta rashin samun tallafi.

Aminiya: Za mu so sanIn tarihin rayuwarka a takaice

Asaki: An haife ni a Unguwar Tudun Bojuwa da ke Kurna a Karamar Hukumar Dala, wanda daga baya muka koma Tudun Fulani. Na yi firamare a nan Makarantar Kurna Gobirawa sannan na yi sakandare dina a Makarantar G.G.S.S Durumi. Daga nan na ajiye na shiga harkar waka koda yake kafin na shiga harkar waka ina yin sana’ar hannu ta rini ina kuma sayar da shaddodi wanda nake ci gaba da yi har yanzu.

Aminiya: Yaya aka yi ka shiga harkar waka?

Asaki: Zan iya cewa na fara harkar waka a dalilin soyayya ne, lokacin da nake soyayya da wata yarinya. Kin san idan soyayya tana dadi, mutum zai rika samun shauki har ya kai yana yabon masoyiyarsa. Sai ya zamanto idan muna waya sai na rika yi mata waka, ita da kanta tana yaba wakar cewa wakar ta yi dadi da sauransu. A haka dai har ya kasance idan na yi wakar sai na je situdiyo na buga ta.

Aminiya: Kafin ka fara soyayya, shin dama can kana gwada wakokin?

Aminiya: Eh, gaskiya ina yi. Sannan kuma ya kasance ko da a cikin mutane nakan gwada yin waka a wanann lokaci mutane sukan fada min cewa in ci gaba da yi watarana zan iya. Mawakin da ke gabanmu Gambo Khalid zan iya cewa shi ne ya ban gudunmawar fara waka domin a ko yaushe yana nuna min cewa zan iya. Saboda karfin gwiwar da yake ba ni idan na yi sabuwar waka sai na yi masa ya saurara.

A karshen shekarar 2018 na fara zuwa situdiyo. A hankali a hankali tun ban saba ba har yanzu ta kai na kware.

Aminiya: Akan wane jigo ka fi yin wakokinka?

Asaki: Gaskiya galibin wakokina na soyayya ne. Amma kuma yanzu wakar da na yi ta karshe wato ta baya bayannan wakar Hip-Pop ce, wadda muka yi tare da wani abokina Beyodi. Mun yi wakar tare inda ya yi da Yarbanci, ni kuma na yi da Hausa. Bisa al’ada wakar Hip-Hop mutum yakan fito ya kwarzanta kansa ya nuna shi wani ne, to haka muka yi wakar. Haka kuma a wajen aikinmu na rini, idan wani abu ya faru sai kawai na wake shi don a yi raha.

Aminiya: Baya ga daukar wakoki a situdiyo shin ana gayyatar ka taro don yin waka?

Asaki: Eh ana yi. Taro na farko da na je shi ne a Fanshekara, lokacin ma ban fara waka a situdiyo ba. To sai Gambo Khalid ya ce min na je na yi waka, amma kasancewar ba kida a wannna lokacin ban samu dama na yi wakar ba. To Alhamdulilah da shekara ta dawo sai Gambo Khalid ya sake kirana ya ce na je taron kuma da na je na yi wakoki ba ma waka daya ba. Kuma bayan da na yi wata wakata, ni da kaina na hada dan kwarya-kwaryar taro a unguwarmu, inda ’yan uwa da abokan arziki da ’yan unguwa suka halarta, to a nan ne fa aka san cewa na fara waka. Domin a gaskiya lokacin da na fara waka na boye wa mutane ba na so su san na fara wakar, saboda ina ganin kamar mutane za su yi min dariya ganin cewa hannu bai fada ba ko wani abu. To da na yi waka ta biyu su mutanen unguwarmu sun karba kuma sun yaba da abin kuma har a gida aka yi ta yi min addu’a. A yanzu ta kai ana gayyata ta idan ana wani sha’ani a unguwa ina zuwa na yi musu waka. Kuma wani lokacin ma kai mawaki mai tasowa bazaka duba abin da za a baka ba, saboda ka san kana da masoya maza da mata. Idan bikin wani ya zo kai kanka abin kunya ne a ce ba ka je ba duk yadda mutum yake sanka a bikinsa ba kai masa wani abu ba. Gaskiya ina yin iyakacin kokarina na je na yi waka duk inda aka gayyace ni.

Aminiya: Zuwa yanzu wakoki nawa ka yi, kuma ka taba yin albam?

Asaki: To ba zan iya cewa ga yawansu ba amma dai suna da yawa. Maganar albam kuma gaskiya har zuwa yanzu ban yi ba, amma ina sa ran yi saboda masoya suna bukata.

Aminiya: Ana zargin wasu mawakan da yin amfani da kalaman da suka ga dama ba tare da tantancewa ba, ya kake ganin haka?

Asaki: To gaskiya ni dai ban dauki wannan wani abu ba domin na yi alkawarin indai sai na yi batsa a waka mutane za su saurara to sai dai ka da a ji wakar, domin ni ba zan yi ba. Ni duk wakokin da na yi ba wadda nake shayin ’yan uwana su ji ko iyayena su ji da ’yan unguwa saboda ba na amfani da duk wani abu da ya shafi batsa. Kamar yadda na fada a baya ina samun shawarwari akan harkar waka daga wajan Gambo Khalid saboda shi yake dorani a kan wasu abubuwa kuma a mafi yawan lokuta ba na yin waka kai tsaye sai ya duba min.

Gaskiya akwai abubwan da nake son yin waka akansu. To sai dai har yanzu ban fara ba. A matsayina na mawaki nakan yi kokari na ga na yi waka kamar a wurin biki ko kuma idan wani ya nemi in masa waka zan yi kokari na ga na yi ba tare da sanya kalaman batanci ba.

Duk da cewa ban taba yin waka akan wasu matsaloli da ke damun al’umma kai tsaye ba, amma zai yi wuya a ce a wakata ban tsarga wani baiti na fadakarwa a ciki ba.

Aminiya: Yaya kake ganin wakokinku, shin suna samun ci gaba a wannan lokacin?

Asaki: Alhamdulillah da wakokin Hip-Hop, da wakokin nanaye yanzu sun samu karbuwa a wajen al’umma saboda ana sauraronsu kwarai da gaske. Mutane da dama suna saurarar waka ba don su ji dadin kida ko wakar ba, sai don jigon wakar ko sakon da ke ciki wanda sai da na fara harkar waka na fuskanci hakan. Mutane na jin abin da ka fada kuma yana tasiri a wajensu. Kin ga ke nan bawai kidan ko wakar ake saurara ba, har da sakon da ke cikin wakar wanda hakan ke sa mutun ya rike wani bangare ko ma baiti. Sai ka ji ana kiran mutum da shi. Hakan yana nuna cewa ana sauraron wakokin.

Aminiya: Yaya kake hangen bunkasar waka gaba daya?

Asaki: A ganina bunkasar wakoki ya shafi yadda take a wurinka. Saboda za ka duba ka gani wane da yayi wakar nasara ya ci ko faduwa ya yi. Saboda ni ban taba ganin waka a matsayin abin da idan mutum ya yi Allah ba zai taimake shi ba ko ba zai ci nasara a rayuwa ba. Saboda lokacin da na fara waka na fadi cewa na dauke ta sana’a. Misali dabanci ko shaye-shaye za ki duba ki gani mutanen da suka yi, riba sukaci ko faduwa. To amma irin harkar waka ko su fim za ki ga mutane da yawa sun samu riba a rayuwarsu sun yi suna kuma sun samu duk wani abu da za su rufawa kansu asiri. Don haka ina sa ran za mu ci ribar waka a rayuwa in sha Allah kuma za mu yi nasara.

A karshe kirana ga gwamnati a rika taimakawa ba ma mawaka kadai ba, hatta irin masu kwakwalwa ta kikkire-kikkire duba ga yanayin kasar ana bukatar hakan. Duk mutumin da ke da baiwa a taimaka masa saboda idan ya zama wani shi ma zai taimaki na kasa da shi. Kin ga kasar za ta zama tana samar da wani abu da za a iya fitar da shi kasar waje su ji ko su gani wanda zai iya jawo a samu kudin shiga a ganina.