Da Dumi Dumi

Akwai hukuncin Allah- Abba Gida-gida

Abba K. Yusuf
Abba K. Yusuf

Dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan Jihar Kano da ya gabata, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce bayan shara’ar Kotun Koli, akwai kuma sha’rar Allah.

Abba ya yi wannan jawabin ne a matsayin martani ga shara’ar Kotun Koli, inda ta tabbatar da zaben Gwamna Ganduje a matsayin Gwamnan Jihar Kano.

A cewar Abba, “hukuncin yau na zaben Gwamnan Kano ya kara tabbatar da cewa akwai masu hannu wajen kwacen zaben, wadanda burinsu shi ne wulakantar da dimokuradiyyar Najeriya.

“Ganin kwararan shaidu da kwararrun lauyoyi suka gabatar, mutum sai ya kasa fahimtar yadda wadannan makiya dimokuradiyya za su hada hannu wajen yi wa mutanen Kano kwacen abin da suke so.

“Amma duk da haka, mun ga karshen abin da za su iya yi, sai kuma su saurari hukuncin Allah, wanda ba za su iya canjawa ba,” inji shi, kamar yadda mai magana da yawun yakin neman zabensa, Sanusi Dawakintofa ya sanar.

ADVERTISEMENT
Share