✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Akwai jan aiki a gaban sabon Firayi Ministan Birtaniya’

A shekaranjiya Laraba ce Mista Boris Johnson ya zama sabon Firayi Ministan Birtaniya bayan ya karbi ragama daga hannun Theresa May. A jawabin da ya…

A shekaranjiya Laraba ce Mista Boris Johnson ya zama sabon Firayi Ministan Birtaniya bayan ya karbi ragama daga hannun Theresa May.

A jawabin da ya gabatar bayan an bayyana shi wanda ya yi nasara, Mista Johnson ya yaba wa Theresa May inda ya ce “ Abin alfahari ne yin aikin da na yi a gwamnatinta.”

Mista Boris ya sha alwashin kammala fita daga Tarayyar Turai sannan zai hada kan ’yan kasar tare da cin galaba a kan Shugaban Jam’iyyar adawa ta Labor, Jeremy Corbyn.

Da take jawabi, Kungiyar Tarayyar Turai ta yi gargadin cewa sabon Firayi Ministan Birtaniya, Boris Johnson yana fuskantar lokaci mai cike da kalubale, a yayin da kungiyar ke mayar da martani kan zabensa a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar Conserbatibe.

Mista Johnson yana da kalubale mai jiransa na jagorantar ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai gabanin wa’adin da aka sanya na ranar 31 ga watan Oktoba.

Ya ce yana son ya sabunta tattaunawa kan yarjejeniyar, ya kuma yi watsi da mafi yawan abubuwan da tsohuwar Firayi Minista Theresa May ta shirya a baya.

Amma shugabannin Kungiyar EU sun ce batun cewa a sake tattaunawa ma bai taso ba.

Sai dai sabuwar Shugabar Tarayyar Turai, Ursula bon der Leyen, ta ce a shirye take ta bai wa Birtaniya wata damar ta sake tattaunawar Bredit, idan har Birtaniya ta zo da sababbin dalilai sahihai, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Da take taya Mista Johnson murna, Misis Ursula bon der Leyen ta ce: “Akwai batutuwa daban-daban kuma masu wahala da ake bukatar magance su tare. Akwai kalubale sosai a gabanmu. Ina gani yana da muhimmanci kwarai a gina wata kakkarfar dangantaka saboda hakkinmu ne mu samar da abu mai kyau ga mutanen Nahiyar Turai da kuma Birtaniya.”

Shugaban Amurka Donald Trump ma ya taya sabon Firayi Ministan murna a shafinsa na Tiwita.

Ita ma Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta taya Boris Johnson murna, tana mai cewa za ta ci gaba da ganin an samu “kyakkyawar” dangantaka da Biratniya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yaba wa tsohuwar Firayi Minista Theresa May kan yadda “ta nuna dattaku da kwarin gwiwa” da kuma yadda ba ta taba “kawo tsaiko ga ayyukan Tarayyar Turai ba.”

Sannan ya ce yana fatar yin aiki da sabon shugaban kan batun ficewar kasar daga Tarayyar Turai da kuma sauran batutuwa masu muhimmanci.

Jam’iyyar Conserbatibe ta Birtaniya ce ta zabi Boris Johnson a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar, inda hakan ya sa ya zama sabon Firayi Ministan kasar.

Mista Boris ya yi nasara a kan abokin takararsa, Jeremy Hunt da kuri’a dubu 92 da 153, yayin da Hunt ya samu dubu 46 da 656.

Theresa May ta taya Johnson murna, inda ta yi alkawarin ba shi goyon baya.