✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai kalubale gaban ‘yan Jarida na Najeriya – Farfesa Pate

Shugaban Tsangayar Koyon Aikin Jarida na Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Umaru Pate ya bayyana cewa, akwai kalubala mai yawan gaske da ke gaban…

Shugaban Tsangayar Koyon Aikin Jarida na Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Umaru Pate ya bayyana cewa, akwai kalubala mai yawan gaske da ke gaban ‘yan jarida da kuma gwamnatoci wajen cimma muradan aikin jaridar yadda ya kamata. 

Farfesan, wanda ya ciri tuta a fagen koyar da nagartattun hanyoyin aikin jarida a Najeriya, ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a wajen wani taron bunkasa aikin jarida a Najeriya da ya gudana a garin Gombe. Ya ce zamanin yin abin da dan jarida ya ga dama ya wuce, yana mai cewa, idan ba a sake lale ba, to za a wayi gari ya zama an rasa masu sauraro anan gaba, sannan kuma hatta masu tallace- tallace su kaurace mu su, abin da zai iya durkusar da kafofin sadarwar da suke yi wa aiki baki daya.

A bangaren gwamnati kuma, Farfesa Umar Pate ya ce, illar rashin inganta kafofin sadarwar shi ne, mutane za su rika sauraron rediyo mai jini dake yayata labaran karya, wanda zai iya jefa al’umma cikin rudani.

Haka zalika wasu kwararru a zauren taron, sun bayyana cewa idan aka fuskanci matsaloli da dukkan kalubalen da suka dabaibaye aikin, to ko shakka babu kafofin yada labarai na nan cikin gida Najeriya suna iya bugun kirji a gaban takwarorinsu na kasashen duniya da a halin yanzu suka fi su kwarjini.

Bugu da kari masu kula da lamura sun bayyana cewa, tuni kafofin sadarwa suka fara yunkurowa wajen samar da labarai masu sahihanci a kan lokaci, tare kuma da kyakkyawan amfani da na’urorin zamani.

Sai dai kuma sun ce ba za a iya cimma wannan burin ba sai gwamnatoci sun zage damtse wajen samar da yanayin da ya dace da kuma kayan aiki da zai ba jama’a zabi.