✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai masu kokarin kawo wa APC ta Katsina matsala da ke Abuja – Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya yi zargin cewa akwai wadansu ’yan siyasar Katsina da ke zaune a Abuja da suke amfani da…

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya yi zargin cewa akwai wadansu ’yan siyasar Katsina da ke zaune a Abuja da suke amfani da karfin Gwamnatin Tarayya domin kawo wa APC matsala a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar daga kananan hukumomi 34 na jihar, inda ya ce wadannan ’ya’yan APC da ke buga siyasarsu a waje sun yi ta kokarin jefa jam’iyyar da gwamnatinsa cikin wani hali. Alhaji Aminu Masari ya ce jam’iyyar tana bukatar garambawul domin abubuwa su tafi yadda suka kamata.

Gwamna Masari ya ce rashin bin doka na iya kawo karshen APC. “An kai bangaren APC na Jihar Katsina da gwamnatina kara gaban kotu sau biyu wanda doka ta tanadi cewa duk wanda ya yi wa jam’iyya wannan a kore shi. Sau biyu ana kai mu Kotun Daukaka Kara”

Gwamnan ya ce “Ana amfani da kudin Gwamnatin Tarayya wajen yakarmu, kuma har yanzu da su ake amfani, mun san abubuwan da suke faruwa. Muna nan, wadanda suka rasa zaben fitar da gwani a 2015 har yau ba su shigo cikin Katsina ba. Ba za mu kyale su, su kawo mana matsala ba a siyarsarmu da mulkinmu.”

“Wadannan mutane ne suka hada kai da PDP a Kotun Karar Zabe domin a rusa nasararmu. Kuma su ne suka buga katin shaidar jam’iyya miliyan biyu domin kawo rikici a zaben fitar da gwani.”

Wani Jagoran APC a jihar, Bala Abubakar, ya tabbatar da haka inda ya ce za su kori wadannan ’yan siyasa daga APC. “Za su iya zama ’ya’yan APC a Abuja, amma ba a Katsina ba,” inji Bala.