✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai rainin wayo a batun garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna – Shehu Aljan

Alhaji Shehu Musa, wanda aka fi sani da Aljan, wanda kuma ya dade wajen aikin tsaro na sa-kai, wanda kuma ya kware wajen kama ’yan…

Alhaji Shehu Musa, wanda aka fi sani da Aljan, wanda kuma ya dade wajen aikin tsaro na sa-kai, wanda kuma ya kware wajen kama ’yan fashi da makami da barayin shanu da kuma masu garkuwa da mutane, ya ziyarci Aminiya a ofishinta da ke Abuja kuma ya yi wa jaridar cikakken bayani game da tushen matsalar garkuwa da mutane a Arewa da kuma hanyoyin da za a magance ta:

 

Ko za ka fada mana aikin da kake yi?

Tun da farko dai an haife ni a Jagindi-Gari da ke Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna amma na girma ne a Karamar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi. Ina kama barayin shanu da ’yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane. Ina aiki kafada da kafada da jami’an tsaron kasar nan. A cikinsu babu wanda bai san ni ba.

Ga shi mun gan ka mutum amma ka ce sunanka Aljan ko ina ka samo wannan suna?

E, wannan wani dogon tarihi ne wanda ya samo asali tun daga wani taimako da na yi wa wani dattijo dan kimanin shekara 90 da doriya a garin Kumasi da ke kasar Ghana, inda sa-in-sa ta hada shi da wasu fasinja a mota har abin ya kai ga fada. Ni kuma daga bisani sai na ce duk fasinjan su sauka sannan na biya kudin motar gaba daya na ce a je a kai shi inda zai je, sannan kuma na saya masa abinci da lemun kwalba. Da za mu rabu duk da yake ban taba ganinsa ba sai ya kira sunana da na mahaifana sannan ya ce daga yau ba sunanka Shehu ba sunanka Aljan. Da na tambaye shi don me sai ya ce kada in damu zan sani. Daga nan kuma ya ci gaba da cewa daga yau duk inda na ga mai laifi in kama shi babu abin da zai same ni. Alhamdulillahi ga shi yanzu na share wajen shekaru 20 ina wannan aiki na kama barayi tare da jami’an tsaro

Ko’ina ka shiga aka daina jin duriyarka sosai duk kuwa da yake akwai kalubalen tsaro musamman na garkuwa da mutane da ake fuskanta a sassan Arewacin kasar nan?

Abin da ya sanya ka ga da ni da su Ali Kwara da Sarkin Bakan Gwambi duk muka yi sanyi, shi ne saboda duk abin da muke yi ba mu gwaninta wajen gwamnati.

Kamar ya ya fa?

A’a, to ka kwashi ’ya’yan mutane kun je kun fuskanci barayi kun fafata bayan Allah Ya ba ka nasara ka kama su ka bai wa ’yan sanda su kuma sun yi talla, sannan kai kuma gwamnati ta kyale ka babu wani tallafi?

In na fahimce ka, kana nufin gwamnati ba ta ba ku tallafin ko sisi ke nan?

A to, in gwamnati ta taba ba mu ko sisi ta fito ta rubuta cikin jarida ta ce ta ba Aljan kudi milyan kaza don ya yi aiki wuri kaza. Wallahi yanzu haka akwai wani gari da muka yi aiki har yanzu ba mu gama biyan bashin kudin tuwon da yarana suka ci ba. Na rantse maka da Allah duk kudin da muke kashewa a aljihuna suke fitowa sai kuma wani sa’in talakawan garuruwan da muka je aiki suna dan tara mana tallafinsu.

Ko wadanne ayyuka ka yi na baya-bayan nan?

Na yi ayyuka da dama. Ni na fara fasa dabar Birnin-Gwari, a lokacin wannan Sufeto-Janar na’Yan Sanda na kasa na yanzu, lokacin yana matsayin DC a Kaduna. Mun yi aiki tare muka kama manyan ’yan fashi da ake cewa ba sa kamuwa. Na kamo har da Nakutama wanda da muka kama shi ya zo mana da bindigogi. Kuma ni na hana fashi da makami a kan hanyar Jos da Binuwai. Sannan kuma kimanin wajen shekaru 4, ni na kama wadanda suka yi garkuwa da maman Mataimakin Gwamnan Taraba. Amma maimakon ya kira ni ya ce mini Aljan sannu da kokari ko ya yaba mini, har yanzu ko sannu bai taba ce mini ba.

Kuma ya san kai ka kama su?

Ya san ni na kama su sosai kuwa. Sannan kuma ga wadanda muka yi karo da su a Zuba, na kama su da makamansu. Ban da maganar shanu da sauransu.

Me kake ganin ya sanya matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa a yankin Arewa?

Ka ga akwai wasu mutanen da ake kira ’Yan Caji Da Beli, wato wadanda suna nan zaune ba su da wata sana’a sai dai idan sun ji an kama ’yan fashi ko masu garkuwa da mutane su je su samu kungiyoyinsu su karbi makudan kudi su je su shiga su fita a tsakanin ’yan sanda da alkalai su ba su kudi su yi belin masu laifin, domin suna da lauyoyinsu. In dai ana son kawar da matsalar tsaro a Arewa to kuwa sai an yi maganinsu. In ba haka ba aikin banza ne ake yi, domin na sha kama barayi bayan ’yan kwanaki sai in ji an sake su kuma ka san komawa za su yi su ci gaba da sata, tun da sun san ko ma me suka yi sakinsu za a yi.

To me za ka ce game da matsalar garkuwa da mutane da ta tsananta a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a halin yanzu?

Matsalar garkuwa da mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna wannan ai rainin wayo ne, domin kuwa idan ka baro Kaduna zuwa Abuja da rana za ka samu motocin ’yan Sanda sun fi 30 amma kuma sai da dare a zo a tare hanyar a harbi mutane sannan a kwashi mutane a shiga jeji da su babu wanda ya kawo masu dauki. Sannan kuma daga baya a zo a kira waya a kai kudi a sake su.

Akwai damuwa fa. Ta ya ya za a ce masu kama mutanen nan har suna amfani da waya su kira ’yan uwan wadanda suka kama kuma a ce wai ba a iya kama su ba?

To, a ina matsalar take ne takamaimai?

Su ma a jami’an tsaron aikin da aka ce ana yi kawai duk karya ake yi. In aka ce maka aikin za a yi ai za a yi. Sannan kuma mafi yawa matsalar na nan a kauyukan da suke a kan hanyar. Mafi yawan mutane nan da suke a wadannan kauyuka ‘informants’ ne na barayi. Sun san lokacin da ’yan sanda suke gama aikin rana da kuma lokacin da wasu za su karba su fara aikin dare. Don haka take sai su sanar da masu garkuwa da mutane, sannan ko shanun da ake sata ana kai wa Fatakwal da sauran wurare ai da tireloli ake daukar su. Bafillatani yana da tirela ne? Sannan kuma ka ga Mahauta su ma suna nan suna jiran a kawo masu shanun satar.

To kana nufin dai masu hannu a cikin wannan badakala suna da dama?

kwarai kuwa, ai shi ya sanya ko an dauko aikin gadan-gadan sai ka ji shiru, domin idan aka ce aikin za a yi to kuwa za a sha mamaki don sunayen da za a gani na manya na da yawa. Ai ko masu garkuwa da mutanen nan ma gadi ake ba su, Tun da za ka iske mai garkuwa da mutane ko takalmin kirki ba ya da shi. Akwai manyansu suna nan zaune a cikin gari.

To gaba daya mene ne za a yi don a yi maganin wannan matsala?

Kasan maganin wannan hanyar ta Kaduna irinmu, ba wai sun ce su bindiga ba ta kama su ba? To ai Ayar Allah na kama su. Mu in aka ba mu hanyar sai mu ce ma ’yan sandan su koma su zauna, ka gani. Abin da ya kamata shugaban ’yan Sanda ya yi shi ne, kirawo irinmu mu hadu da Buratai sannan a kai mu gaban Shugaban Kasa mu zauna ya fada mana irin gudumawar da ake so mu ba da mu kuma mu fada masa wuri kaza ga irin matsalar da ake da ita ga yadda kuma za a magance ta. Sannan kuma wannan aiki ne na infoma da za a samar wadanda suke a wurin da matsalar take faruwa wadanda za su shiga ciki sosai ba tare da jin tsoro ba gwamnati ta biya su hakkinsu, su kawo mana bayani. Ba irin tsarin da ake amfani da shi a yanzu ba wanda infoma zai kawo bayani a kama masu laifi shi kuma a sake su. Sannan su zo su fada masa cewa sun san cewa shi ne ya ba da bayani game da su daga karshe kuma su kashe shi.