Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Akwai riba a kiwon kajin gidan gona

Wani manomi mai kiwon kajin gidan gona, Mista Emmanuel Iregbeyen, ya ce kiwon kajin gidan gona akwai albarka a cikinsa, muddin mutum yana da jari da kuma kwarewa kan yadda za a yi.

Mista Iregbeyen, mamallakin kamfanin gidan gonan nan na Emiraz, da ke harkar kiwon kajin, shi ne ya bayyana hakan a wata hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai  na Najeriya (NAN) a Jihar Legas.

ADVERTISEMENT

Ya ce kiwon kajin gidan gona nan, na bukatar gwaggwaban jari da kayan aiki, ya kasance kuma mutum ya sa mu horo na yadda zai gudanar da harkar, zai samu riba mai yawa.

“Idan Manomin kajin gidan Gona ya kasance yana da jari a lokacin da zai fara Noman zai samu gwaggwabar riba”. inji Iregbeyen.

ADVERTISEMENT

Da jarinka mai karfi, idan ka shiga harkar Noman kaji za ka samu nasara a kiwon, a kalla a ce ka mallaki fili ka gina, ka sayi kaji, ka zuba kafin ka fara zuwa wani lokaci za ka ga yadda za ka samu alkhairi.

Duk wani da yake da kwarewa a bangaren kasuwanci, zai iya shiga harkar Noman kajin gidan Gona, idan yana da kwararru da za su dinga ba shi shawari kan yadda zai gudanar da Noman Kajin. Inji shi.

Mista Emmanuel da yake magana akan cutar kajin, kasancewar ita ce babbar kalubalen kaji idan ana musu rigakafi suna samun magani, matsakaicin manomi zai kai labari.

Ya kara da cewa, wani kalubalen har yanzu da manoman kajin gidan Gona ke fuskata shi ne akwai yawan mutuwar kajin, idan annobar cutarsu ta bulla.

Sannan kuma mafi yawancin cutar kajin akwai rigakafin cututtukan. Sai dai murar kajin ne ba ta da magani, gwamnati kuma ba ta barin manoman su yi musu rigakafi. Inji Kwararren Kiwon Kajin.

Ya kara da cewa, kananan manoman kajin basa iya wadatar da al’umma da yawan naman kajin da ake bukata.

Sai yace idan suka samu tallafi daga gwamnati, sa’annan aka samu jama’a suka dukufa a harkar Noman kaji, to za su iya wadatar da Naman kaji da ake bukata ga ‘yan Najeriya.

“Muna da dubban wadanda suka kammala karatunsu na digiri a jami’oi, ba su da aikin yi idan aka koya musu yadda ake kiwon kajin gidan Gona na Nama wato ‘broilers’ hakan zai sa a samu wadatuwar naman da ake bukata.

Sa’annan yace mutane na bukatar horo, dan samun dama na ci gaba da samar da kaji da zarar mutane na karuwa a harkar da taimakon gwamnati manoman za su iya dawowa kamar a da, wajen safarar naman kaji. Inji shi.