Search
Subscribe
Akwai rufin asiri a sana’ar gasa kaji da Salwa – Ahmed Meku

Ahmed Meku Maikaji da Salwa

Akwai rufin asiri a sana’ar gasa kaji da Salwa – Ahmed Meku

Ahmed Meku Maikaji da Salwa Jos, fitaccen mai sana’ar gasa kaji da salwa da tsire da dambun nama ne a garin Jos, fadar Jihar Filato. A tattaunawa da wakilinmu, ya bayyana yadda koyi wannan sana’a da irin nasarorin da ya samu, inda ya ce akwai rufib asiri a sana’ar:

A wane lokaci ka fara wannan sana’a?

To ita wannan sana’a na fara koyonta ce a wajen mai gidana, Alhaji Sani Standard  Jos. Shi ya koya mini sana’ar gasa kaji da salwa da tsire da dambun nama da kilishi. Kuma na yi kamar shekara 10 ina tare da shi. Daga nan na  bude wannan waje  a shekarar 2017.  A  wannan wuri muna gasa salwa da kaji da tsire, muna  kilishi, wanda har oda ake yi daga garuruwan Fatakwal da Legas da Ibadan.

 

Wadanne nasarori ka samu a wannan sana’a?

A gaskiya na samu nasarori da dama, domin a  yanzu ba ya ga wannan wuri da nake wannan sana’a, na bude rassa  a wurare biyar a nan garin Jos.  Wuraren da na bude sun hada da  Atili Street da Ibrahim Taiwo da Sakatariya da Katako Junction da Gidan Man Jagab.  Kuma ina da yara sama da 10 da muke aiki da su a wadannan wurare. Kuma ta dalilin  wannan sana’a na yi iyali da muhalli.

 

Wane muhimmanci kake ganin wannan sana’a take da shi?

Gaskiya akwai rufin asari a wannan sana’a ta gasa kaji da salwa. Domin idan har Allah Ya sa maka nasibi za ka samu abin da za ka ci kuma ka ciyar da iyalanka. Domin Allah Ya yi wa wannan sana’a albarka.

 

Mene ne babban burinka kan wannan sana’a?

Babban burina kan wannan sana’a shi ne in ga cewa na bude rassa a jihohi daban-daban na kasar nan. Yanzu har na fara shirin bude wuri a garin Kaduna.

 

Karshe wane kira kake da shi ga matasa game da muhimmancin sana’a?

Ina kira ga matasanmu su tashi su kama sana’a domin su kare mutuncinsu. Rashin sana’a ga matasa yake sawa ana yaudararsu da ’yan kudade kalilan suna zuwa suna aikata abubuwan da ba su dace ba. Amma idan matasa suna sana’a babu yadda za a yaudare su su je su aikata abubuwan da ba su kamata ba. Don haka sana’a tana da matukar muhimmanci ga matasa. Kuma ina kira ga iyaye su rika kokari suna sanya ’ya’yansu a wuraren koyon sana’o’i tun suna kanana, ta yadda za su taso da iya sana’a.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin