✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yaudara a kan kafa kwamitin sulhu da ’yan Boko Haram – Walin Kalgo

A watannin baya Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin sasantawa da kungiyar Boko Haram, wakilinmu ya tattauna da Alhaji Abubakar Atiku Walin Kalgo wani tsohon babban…

A watannin baya Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin sasantawa da kungiyar Boko Haram, wakilinmu ya tattauna da Alhaji Abubakar Atiku Walin Kalgo wani tsohon babban limamin sojoji kan lamarin:

Aminiya: Me kake ganin shi ne musabbabin kungiyar Boko Haram a Najeriya?
Walin Kalgo: Akwai abubuwa da dama da suka zamo musabbabin samuwar Boko Haram. Na farko rashin yi wa talakawa adalci daga shugabanni. Shugabanni suna ta kwashe dukiyar kasa daga su sai iyalansu, kuma talakawa su ne sanadiyyarsu zuwansu kan mukaman da suke rike da su. Kuma akwai rashin aikin yi ga matasa birni da kauye. Wata babbar matsala kuma, koda an sasanta da ’yan Boko Haram, to idan Allah Ya kai mu shekarar 2015 aka yi zabubbuka idan hukumar zabe ba ta tsaya a kan gaskiya ba, wanda ya ci zabe a ba shi, wallahi tallahi kungiyar da za ta bulla sai tafi ta Boko Haram barna. Domin jama’a sun wahala tun lokacin yin rajista da kada kuri’a, lokacin zabe wadansu mata ma har nakuda ta kama su a kan layuyyukan zabe, saboda cimma burinsu na su zabi wanda suke so. Amma hukumar zabe ta kasa ta yaudare su, ta ki ba su wadanda suka zaba. Idan har hukumar zabe ta sake maimaita abin da ta yi a shekara 2011 na rashin ba jama’a wanda suka zaba, to sai dai mu ce Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.
Aminiya: Kana ganin afuwa ita kadai ce mafita ga rikicin ’yan Boko-Haram?
Walin Kalgo: To, ina ganin wannan hanya ita ce kadai mafita, dalilina na cewa a yi wa ’yan Boko-Haram afuwa shi ne saboda ganin yadda kasar ta zama kusan kowa ya fara gane cewa karfin tuwo kawai ba zai kawo karshen abin ba.
Na farko dai an yi wa ’yan kungiyar OPC afuwa da kuma ’yan Neja-Delta. Kuma su ma abin da suka aikata har ya fi na wadannan, to in dai ba akwai wata manufa ba, ya kamata su ma wadannan a yi sulhu da su. Yin afuwa yana da tarihi a zaman Najeriya. Domin a lokacin da aka yi Yakin Basasa a kasar nan, bayan yakin Gwamnatin Tarayya ta yi wa wadanda suka yi tawaye afuwa, kuma sojojin da suka yi yaki a gefen ’yan tawayen an dawo da su cikin rundunar sojojin Najeriya. Kuma aka biya su albashin watannin da suka yi suna yaki a gefen ’yan tawaye. Bayan haka, a lokacin marigayi Shugaban kasa Alhaji Umaru Musa ‘Yar’aduwa ya yi wa ’yan kungiyar tsagerun Neja-Delta afuwa. Wadannan tsageru sun yi kashe-kashe, sun yi garkuwa da mutane, an yi asarar  rayuka masu tarin yawa sakamakon wannan tawaye. Sojoji sun yi shekara da shekaru suna amfani da karfi kan wadannan tsagerun, amma ba a samu biyan bukata ba. Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi amfani da karfin soja amma ba a samu biyan bukata ba. Amma marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa a cikin hikimarsa ya yi wa wadannan ’ya’yan talakawa afuwa kuma aka samu zaman lafiya a wannan yanki. Saboda haka matsalar nan ta Boko-Haram kusan shekara biyar ke nan ana fama da ita a kasar nan. An kai jami’an tsaro an girka a ko’ina arewacin kasar nan, kowace unguwa akwai soja kowane kwararo akwai soja, amma an kasa magance wannan matsala. Hare-haren da ake kaiwa ya ma fi wanda ake kaiwa a lokacin da aka fara kai hare-haren. Wannan ya nuna cewa nuna karfi ba zai biya bukata ba.
Aminiya: Me za ka ce game da kwamitin da aka kafa domin sasantawa da ’yan Boko-Hram?
Walin Kalgo: To akwai wata yaudara da kafa wannan kwamiti ta bangaren Gwamnatin Tarayya. Dalili kuwa shi ne bayan an kafa wannan kwamiti, bai riga ya gama aikinsa ba, sai kawai Shugaban kasa ya kafa dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe har da Adamawa wadda ba ta da rikicin Boko-Haram sosai, kuma abin bakin cikin bayan an kafa musu dokar ta-baci sai aka kuma mamaye jihohin da tankokin yaki da sojoji. karin bakin ciki kuma aka yanke dukkan hanyoyin sadarwa na jihohin uku, wato sojoji su ci karensu babu babbaka, ba a samun labarin irin halin da jama’ar jihohin suke ciki.
To ka ga kwamitin da gwamnati ta nada ya zama shirme, domin wadanda za a zauna da su a sasanta an tura musu sojoji ana farautar su da su da matansu da ’ya’yansu. Idan gwamnati da gaske take yi na a sasanta da ’yan kungiyar Boko-Haram, bayan an yi masu afuwa duk wanda suka samu rauni ko aka rushe musu gidaje ko coci-coci ko masallatai, Gwamnatin Tarayya ta fitar da kudade don a taimaka musu, a kuma saki matansu da ’ya’yansu da ke tsare. Yin haka zai kawo hadin kai, zai sanya a manta da abubuwan da suka faru. Kuma gwamnatin ta tuna bayan ’yan Boko-Haram akwai ’yan Boko Halal masu hana ruwa gudu, wadanda suke cin abinci da sunan wannan rikici, suna nan suna ta kaiwa da komowa don yi wa wannan shiri zagon kasa, domin a wurinsu idan har aka samu zaman lafiya, to, ba karamar asara za su yi ba. Wadannan mutane akwai su a jami’an tsaro, akwai su a cikin malaman addinin Musulunci da addinin Kirista, akwai su a cikin ma’aikatan gwamnati.
Wadannan mutane burinsu kawai shi ne a ci gaba da jefa bama-bamai su kuma su ci gaba da kwashe kudaden kasa da sunan tsaro. Ina kira ga ’yan Najeriya mu tashi mu fallasa irin wadannan mutane domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Saboda irin wadannan mutane su ne munafukan kasar nan.
Aminiya: A karshe mece ce shawararka ga ’yan Najeriya?
Walin Kalgo: Ina tausaya wa mu ’yan Najeriya kan halin kunci da muka shiga, ina rokon Allah Ya kawo mana sauki kan wannan hali da muka shiga. Kuma ina kira ga shugabanninmu suji tsoron Allah, su tuna za mu mutu komai dadewa. Ina kuma kara tunatar da hukumar zabe ta kasa cewar Allah ya ce duk wanda aka zalunta daidai da kwayar zarra sai Ya saka masa, to jama’ar hukumar zabe ku yi hankali, ku tuna da ranar Hisabi, ranar da mai malkwasassar hula ba ya iya cetonku, daga kai sai halinka.