✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar Iran ta yi kuri’a game da nukiliyarta

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ba da bayyana cewa watakila Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta gudanar da kuri’ar raba gardama a kan shirin…

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ba da bayyana cewa watakila Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta gudanar da kuri’ar raba gardama a kan shirin nukiliyar kasar, a daidai lokacin da zaman tankiya ke kara yawaita a Yankin Gabas.

Karamin kamfanin dillancin labarai na kasar, ILNA, ya ruwaito Rouhanin yana cewa sadara ta 59 na kundin mulkin kasar watau “kada kuri’ar raba gardamar” shi ne zai warware duk wata kiki-kakar shirin nukiliyar tare da zama mafita daga matsalar.

Jawabin hakan na zuwa ne bayan shugaban addinin Iran din Ayatollah Ali Khamenei ya yi wata kakkausar suka ga shugaba Rouhani a bainar jama’a, akan yadda shugaban yake shiriritar da yarjejeniyar shirin nukiliyar kasar cikin gaggawa.

A makonnin da suka gabata, Mista Rouhani ya mayar da martani akan sabon takunkumin karya tattalin arzikin kasar da Amurka ta kakaba mata, ta hanyar yin barazanar cewa Iran din na iya janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimmawa a shekarar 2015, wanda dama Amurkar ta riga ta fice daga yarjejeniyar tun bara. Sai dai wannan matakin ya kusan jefa kasar Iran cikin kazamin yaki da Amurka.

Tun lokacin da shugaban Amurkar, Donald Trump ya janye kasarsa daga yarjejeniyar, gwamnatin Amurkar ke kara matsi akan Iran din ta hanyar toshe kafofin fitar da man fetur din Iran zuwa kasuwannin duniya, wanda hakan ya kara rura wutar dadadden zaman tankiyar dake a yankin.

Da take kafa hujja a kan wata barazana ga rundunoninta da ba ta ambata ba a yankin na Gabas ta Tsakiya, Amurkar ta tura katafaren jiragen ruwanta na yaki da kuma samfurin wasu jiragen jefa boma-bomai samfurin B-52 zuwa yankin tekun Pasha, tun farkon watan nan wanda hakan ya kara rura wutar yiyuwar barkewar yaki. Sai dai hukumomin birnin Tehran din sun bayyana jibge dakarun da Amurkar ke yi a zaman taken-taken yaki kuma ta na siyasantar da abin.

Yayin da da daman mahukuntan Iran din ke kekasa kasa cewar ba sa muradin fara yaki da Amurka, daya bangaren sukar manufofin shugaban kasar a bainar jama’a da shugaban addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei ke yi na nuni ne da irin matsayinsa na neman a gwabza yaki tsakanin kasashen biyu.

Ayatollah Khamenei dai ya sha fadin cewa wakilan kasar a tattaunawar shirin nukiliyar Iran din suna yin saku-saku sosai a yarjeniyoyin da ake kullawa.

Yunkurin kada kuri’ar raba gardamar da shugaba Rouhanin ya gabatar ka iya taimaka masa wajen warware takaddamar shirin nukiliyar ba tare da ya rasa kimarsa ba a idon ‘yan kasar, yana kuma iya taimaka masa a siyasan ce akan duk irin shawarin da masu zabe za su iya dauka.

A fili take cewar al’ummar kasar na goyon bayan yarjejeniyar shirin nukiliyar da kuma tasirin da take dashi ta fuskar bunkasar tattalin arzikin Iran din. Sai dai masu kudin kasar da alama sun ji jiki matuka sakamakon takunkumin shekara da shekarun da aka kakabawa kasar tare da karyewar darajar takaddar kudin kasar.

A baya dai Iran din ta gudanar da kuri’ar raba gardamar sau uku tun bayan Juyin Juya Halin Kasar na shekarar 1979. Na farko ta yi shi ne akan ‘yan kasar ko sun amince da Juyin Juya Halin kafa Jamhuriyar Musulunci a kasar, sai kuma na biyu da aka yi akan neman sahalewar ‘yan kasar game da sauya kundin mulkin kasar.

Mista Rouhani ya ce ya gabatarwa da shugaban addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei shawarar kada kuri’ar raba gardamar akan shirin nukiliyar a shekarar 2004, yayin Mista Rouhanin yak e cikin ayarin masu tattauna samar da yarjejeniyar shirin nukiliyar kasar.