Da Dumi Dumi

Akwai yiwuwar Jam’iyya APC za ta amshe mulkin kasar nan a shekarar 2015 – Sule Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce babu shakka Jam’iyyar APC za ta iya fitar da Jam’iyyar PDP daga kan karagar mulki a shekarar 2015 saboda abin da ya kira PDP tana wasa da damarta.
Gwamna Lamido ya bayyana haka ne a lokacin da kakakin tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibarhim Shekarau, Alhaji Sule Ya’u Sule ya ziyarce shi a Gidan Gwamnatin Jihar lokacin da ya jagoranci tawagar kungiyar Jami’an Hulda da Jama’a (NIPR) reshen Jihar Kano a ranar Litinin da ta gabata.
Gwamna Lamido a baya ya taba cewa Jam’iyyar PDP ce za ta ci gaba da mulkin kasar nan sai dai ya ce
muddin PDP ta ci gaba da rashin kintsa kanta, babu makawa Jam’iyar APC za ta tsinci dami a kala domin babu maka wa ita ce za ta kafa mulki a shekarar 2015 kuma ita ce jam’iyyar da za ta iya ceto kasar nan daga halin da ta fada a ciki.
Gwamna Lamido ya kara da cewa PDP ita ce jam’iyyar da ta ceto Najeriya daga bakin mulki na sojoji da ta yi fama da shi a shekarun baya.

Share