✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar kotun duniya ta ICC ta amince da bukatar AU kan Uhuru Kenyatta

Akwai  yiwuwar Kotun Duniya d ake Hukunta masu aikata miyagun laifuka ta maince da bukatar Tarayyar Afirka, wajen kin amincewa da laifin da ake tuhumar…

Akwai  yiwuwar Kotun Duniya d ake Hukunta masu aikata miyagun laifuka ta maince da bukatar
Tarayyar Afirka, wajen kin amincewa da laifin da ake tuhumar Uhuru Kenyatta da mataimakinsa, ind asuka sdhirya gabatar wa Majalisar dinkin Duniya takardar kin amincewar Tarayyar.
Shugaban Lauyoyin Kenya, Eric Mutua, ya ce wannan amtsaya da Tarayya Afirka ta yanke, tare da barazdanar janyewar kasashen Afirka daga kotun, za su tursasa kotu, ta aiwatar da abin da zai dadada wa wanda ake tuhuma da laifi.
Ya bayyana cewa, tund akasashen Afirka na da fada a aji a kotun ICC, sabod ayawan kasashen d ake cikinta ya kai 34, to bukatarsun ba za ta samu matsala, kuma za su yi tasiri a wajen mai gabatar da kara Fatou Bensouda.
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta yana fuskantakar kalubale daga ’yan majalisar kasar, a kokarins na rage musu albashi, ta yadda zai smau sauki kirkiro sababbin ayyuka. Kenyatta wanda ya lashe zaben 4 ga Maris din bana, ya goyi bayan hukumomin kasar a yunkurinsu na rage albashin ’yan majalisar kasar, wadanda a halin yanzu ke cikin jerin ’yan majalisar kasashen duniya da ke kwasar albashi amfi tsoka.
’Yan majalisar na shirin kada kuri’ar kin amincewa da kudurin shugaban kasar, a wani zama da za su yi cikin wannan makon, inda za su jajirce kan cewa rage albnashin ya saba wa doka.