Da Dumi Dumi

‘Akwai yiwuwar Rasha da Turkiyya sun aikata laifuffukan yaki a Syria

Kungiyoyin Kare Haqqin Dan Adam sun qiyasta cewa mutum dubu 300 zuwa 500 suka hallaka a yakin Syria da ya shiga shekara ta tara
Kungiyoyin Kare Haqqin Dan Adam sun qiyasta cewa mutum dubu 300 zuwa 500 suka hallaka a yakin Syria da ya shiga shekara ta tara

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun zargi Rasha da kashe fararen hula a farmaki ta sama da ta kai bara a kasar Syria yayin da ’yan tawayen da ke kawance da Turkiyya  suka hallaka mutane tare da kwasar ganima a yankunan Kurdawa. Masu binciken sun ce, wadannan ayyuka sun kai a kira su DA laifuffukan yaki da gwamnatocin  Moskow da Ankara suka aikata.

Rahoton wata hukumar majalisar ya gano Rasha, wadda ita ce babbar mai dafa wa gwamnatin Syria a yakin da take yi da ’yan tawaye, ta kaddamar da hare-haren sama kan wata kasuwa mai farin jini da kuma wani sansanin ’yan gudun hijira, wadanda suka haddasa kisan fararen hula da dama a watannin Yuli da Agustan bara.

“A dukkan hare-haren biyu, mayakan saman Rasha ba su nufi farmakin kan kafofi ko muradun soji ba, wanda hakan ka iya zama laifin yaki a kaddamar da farmakin kan mai tsautsayi a yankunan fararen hula,” inji rahoton.

Rahoton ya bayyana take hakkoki da ’yan tawaye masu samun goyon bayan Turkiyya suka aikata a farmakin da suka kai kan yankunan da ke karkashin ikon Kurdawa, inda ya ce, idan dai har ’yan tawayen suna samun umarnin aika-aika daga kwamandojin sojin Turkiyya, to kuwa lallai wadannan kwamandoji sun aikata laifuffukan yaki.

Paulo Pinheiro, wanda shi ne Shugaban Hukumar Majalisar Dinkin Duniyar, ya ce hukumar ta shigar da sunayen wadanda ke da hannu a aikata laifuffukan yakin na baya-bayan nan cikin jerin littafin sunayen wadanda ake zarginsu da aikata miyagun laifuffuka.

ADVERTISEMENT

Hukumar ta karbi bukatun neman bayanai 200 daga hukumomin shari’a a duniya dangane da bayanan laifuffukan da aka aikata cikin shekara tara na yakin na Syria, kamar yadda ya fada wa wani taron manema labarai.

Rahoton ya zargi Rasha kan wani harin sama a birnin Maarat al-Numan a ranar 22 ga watan Yuli inda akalla fararen hula 43 suka mutu. Gidaje biyu tare shaguna 25 aka ruguza bayan da wasu jiragen sama na yaki guda biyu mallakar Rashar suka bar sansanin mayakan sama na Hmeimim inda suka yi wa yankin kawanya, inji rahoton.

Makonni bayan nan, wani hari kan ginin Haas da ke zama matsugunin wadanda yakin ya raba da muhallansu, ya hallaka akalla mutum 20, ciki har da mata takwas da kananan yara shida, tare da jikkata wadansu 40, inji rahoton.

Rahoton ya kuma yi kira ga Turkiyya ta gudanar da bincike ko shin ita ce da alhakin wani farmakin sama kan wani ayarin fararen hula kusa da Ras al-Ain wanda ya hallaka mutum 11 a watan Oktoban bara.

Turkiyya dai ta musanta hannu cikin harin, wanda Hukumar Sa-ido kan Hakkokin Bil Adama ta Syrian (Obserbatory for Human Rights), da ke da mazauni a Birtaniya, ta ce jirgin yakin Turkiyyar ne ya kai harin.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya