✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alamta alamun al’adun al’ummu (2)

’Yan makarantar Dodorido da ke falle shafukan darussan dawurwurin dambarwar kakar zabukan bana, musamman ganin yadda MAGABTAN AL’UMMA ke ta hankoron hargitsa kasa don gudun…

’Yan makarantar Dodorido da ke falle shafukan darussan dawurwurin dambarwar kakar zabukan bana, musamman ganin yadda MAGABTAN AL’UMMA ke ta hankoron hargitsa kasa don gudun kada su ci kasa a zaben shekara ta dubu karamin lauje da sili da muniyar kasa, muna kokarin ganin ’yan makarantarmu sun yi karatun ta-natsu, musamman wajen fitar da muhimman bukatun al’umma. Hakika Baban-burin-huriyya ya yi alwashin bai wa ’yan adawa DAMA SU DAMA, don gudun kada su rankaya cikin kungurmin dawa.

Ko ma dai da wace irin manufa Jam’iyyar tsintsiyar share jibar da aka jibga wa Haurobiya ta kudiri aniyar bai wa ’yan adawa damar damawa, ina ganin akwai bukatar zaburar da su kan muhimman ayyukan tsabtace muhalli, don gudun kada su kara jibga mana jibgin sharar da juji ba zai iya dauka ba.

Alal hakika Haurobiyawa na sane da muhimmancin ingarman inganta kasa da mikiyar falle fuka-fuki sama-sama; tsirin tsuntsu a tsaye cirko-cirko kan makekiyar kasa da ke da manyan mahadan kogunan karamin lauje, duk dai a matsayin tambarin tinkaho da tutiyar kimar darajar Haurobiya ake tallata wa al’ummun duniya. Uwa-uba, tambarin kasar Haurobiya na nuni da ALAMTA ALAMUN AL’ADUN AL’UMMU. Don haka ba wani abin ta’ajibi ba ne idan wata masana’anta ko farfajiyar hada-hadar harhada kan Hauro ko kungiyoyin masu fuka-fukin tashi, ballantana jam’iyyun siyasa, a ga sun alamta manufarsu da TSINTSIYA ko DANBOTO DA SANDA JIRGE ko ZAKARA ko MABUDIN MAGARKAMA da dai makamantantsu.

Kuma wadanda suka dan sha miya bisa kimar nisan shekarunsu a duniya, musamman a kasar Haurobiya suna sane da cewa a JAMHURIYYAR FARIN-FARAWA, wato fafutikar farkon kafuwar DAMON-KURAR DIYA (kodayake lamarin ya rikide zuwa DAMO-DA-KURA-DA-DIYYA a yau), an taba samun jam’iyyu da suka alamta da HAUYA, wato abin fardar GARKAR GAYAUNA don yin artabu da tabahuwa. Kai hasali ma a JAMHURUN JAN RAGAMAR rukunin karamin lauje, AN YI JAM’IYYA MAI GIDA DA MASARA, wadda ta kai ga gaci wajen kafa jagorancin Haurobiyawa a karkashin tsohon Shugaban Haurobiya mai zungureriyar tagiya, lokacin da aka wataya aka SHIGA SHAGALIN SHAN-GARI, har kuma al’umma ta afka cikin GARARIN GARI, inda sakamakon rashin sararin sararawar al’umma aka bullo da tsarin TSUKE LALITAR GWAMNATI. Tabbas idan aka ci gaba da bin kadin ALAMTA ALMUN AL’ADUN AL’UMMU da jam’iyyun siyasa suke dora fafutikarsu a kai za a karke da SURUTU RUTUTU, har a zarta KAMFANIN DILLANCIN LABARAI NA REUTERS.

Batu mafi muhimmanci dai shi ne, idan har FARFAJIYAR KOYON WATSATTSAKE DA BUDA WAGAGEN LITATTAFAI ta Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar Haurobiya ta tallata wa duniya tambari karo da zuge da fekakkiyar gamba, ko tantama babu an san nuni ake yi da himma ka’in da na’in wajen yakar JUHALA don tabbatar da ADALA, don gudun kada al’umma ta yi ta salallamin LALALA. Sannan akan yi kokarin ganin kowa ya bi DOKA don kada al’umma ta KOKA.

Lallai Haurobiyawa mu yi tsaye tsayin DAKA, don ganin kowa ya hau bisa turba, ta yadda babu tababa za mu yi ta yi wa juna HABA-HABA. Saboda haka hakkin kowa da kowa ne tarairayar almajirai, don ceton rai, musamman a lokacin hunturu da ba su da hutu, har ma takan kai ga a ga kolo ko titibiri mai kwazo fatarsa ta yi fururu. Bisa wannan dalilin ganin halin da ’ya’yan ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA ke ciki, muna fatan kowace jam’iyya za ta alamtu da irin tsilli-tsillin matsalolin da ta kafu wajen warware wa al’ummar Haurobiya.

Haurobiyawa babban abin da darasin makarantar nan ke fafutikar nusar da dukacinmu shi ne, wato mu yi CIRKO-CIRKON cike-ciken cikon IMANIN ADDINI, ta yadda kyawawan ta’adun kyautata muhalli da zamantakewar al’umma da muka yi imani da su kowa ya tabbatar ana gudanar da su a tsabtace. Abin dai fahimta a nan kowa ya share gidansa da tsintsiyar kwakwa da ’yar laushi ba tare da tsiya-tsiya ko tsiwa ba. Sannan mu fito da muhimman bukatun al’umma, mu kattaba su a warkokin watsattsake don hana miyagu wadaka; daga nan sai mu tura wa Gwamnatin Baban-burin-huriyya, ita ma kada mu daga mata kafa har sai ta tabbatar da abin da ya dace a aiwatar. Sai dai wani hanzari ba rarewa aguje ba, dole ne kowa ya bayar da irin tasa/tata gudunmawar wajen warware tsilli-tsilin matsalolin da suka dabaibaye al’umma.

Ina mai tabbatar wa Haurobiyawa a kowane fanni na rayuwa idan muka hada karfin karfen karafan titin tarragon kwangirin dogo, ba tare da bata lokacin wulwulawar agogo ba, to tabbatas sai nagartar kasarmu ta karu fiye da :bajintar birnin BEIJING KO FAFUTIKAR FANTMAWAR FARANSAWA DA AMARCIN AMAREN ATTAIJARAN AMURKAWA DA BURUNGUZUMAR BUNKASAR BIRTANIYAWA KO RUGUGIN RARAKAR RAKA-RAKAR ROKAR RASHAWA (amma idan mun daina cin rashawa), uwa-uba da SAUYIN SALON SANSANIN SINAWA. Sai mu kara kwazo wajen yi wa mazaje kozo a wajen tafiya Gwarzo.

Ni dai tuni a nasan GWARZON GWARAZA A WAJEN CIN GWAZA shi ya sa kuka ji ina ta GAZA, FATANA DAI KADA IN GAZA, tare da fatan Mai-duka Mai-kowa, Mai-komai zai yi mana maganin mutanen BANZA, ta yadda za su ga HAZA a banzar bazara; mu dai mu daina nuna wa juna KYARA, wai saboda kawai ZAKARA na CARA ko KAZA ta yi KYARKYARA!