✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alamu sun nuna Arsene Wenger zai koma AC Milan

Ya zuwa shekaranjiya Laraba rahotannin da ke fitowa daga Italiya sun nuna tsohon kocin Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger yana tattaunawa da mahukunta kulob…

Ya zuwa shekaranjiya Laraba rahotannin da ke fitowa daga Italiya sun nuna tsohon kocin Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger yana tattaunawa da mahukunta kulob din AC Milan da ke Italiya don ya fara horar da ’yan kwallon kulob din.

Arsene Wenger wanda ya yi murabus daga Arsenal kafin a fara kakar wasa ta bana, ya shafe kimanin shekaru 22 a kulob din kafin ya yi murabus.

Dan shekara 69 rahotanni sun nuna kulob da dama ne suke zawarcinsa ciki har da na Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa da kuma na Real Madrid da ke Sifen da kuma na AC Milan da ke Italiya.  Sai dai ga dukkan alamu zai sanya wa kulob din AC Milan hannu ne bayan tattaunawa da shi ta yi nisa.

A kwanakin baya ne aka ji Wenger yana fadin ya kusa komawa fagen horarwa, da hakan ta sa kulob da dama suka shiga zawarcinsa.

Idan yarjejeniyar ta kulla Wenger zai maye gurbin kocin Milan na yanzu Genaro Gattuso.

Kawo yanzu AC Milan ce take matsayina hudu a teburin gasar Serie A ta Italiya bayan an yi wasanni 11.