✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alao Akala ne dan takarar Gwamna na ADP a Jihar Oyo

Matsalar da ta tsao a tsakanin masu son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Oyo a karkashin Jam’iyyar APC, ta sa tsohon Gwamnan Jihar, Otumba Christopher Adebayo…

Matsalar da ta tsao a tsakanin masu son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Oyo a karkashin Jam’iyyar APC, ta sa tsohon Gwamnan Jihar, Otumba Christopher Adebayo Alao Akala da dimbin magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar, inda suka juya akala zuwa ga Jam’iyyar ADP, wadda ta ba tsohon Gwamnan tikitin takarar Gwamna a zaben badi.

A jawabinsa a ranar Lahadin da ta gabata bayan karbar tikitin zama dan takarar, tsohon Gwamnan ya umarci dukan magoya bayansa ba tare da bata lokaci ba, su hanzarta tattara nasu ya nasu su fice daga APC, su koma ADP.

Ma’ajin Jam’iyyar ADP na Kasa, Iboro Ige-Edaba da Sakatariyar Tsare-Tsare ta Jam’iyyar, Uwargida Dokta Oliza ne suka wakilci uwar jam’iyyar daga Abuja wajen mika wa tsohon Gwamnan satifiket a babban ofishin  jam’iyyar da ke Ibadan.

Ficewar Cif Alao Akala daga APC ta biyo bayan rashin amincewarsa da  yadda Gwamna Abiola Ajimobi ya gudanar da al’amuran zaben fitar da gwani na jam’iyyar ne, wanda ya ce ba a yi adalci ba ko kadan.

Tun makonni biyu da suka gabata ne jam’iyyun adawa na PDP da ADC da ADP a Jihar Oyo suka fara zawarcin tsohon Gwamnan, bayan ficewar da ya yi daga APC, inda a karshe ADP ta yi nasarar karbarsa.

Bincike ya nuna cewa yanzu haka wadasu ’yan takarar kujerun Majalisar Tarayya da ba su amince da yadda aka yi zaben fitar da gwani a jam’iyyun PDP da APC ba, sun fara yunkurin tafiya tare da Alao Akala inda aka ba su tabbacin samun matsayin da suke nema a ADP.

Tsohon Gwamnan ya taba tsayawa takarar Gwamna a inuwar Jam’iyyar Labour Party a shekarar 2015, inda ya sha kaye a hannun Gwamna Ajimobi na APC. Daga baya a shekarar 2016 tsohon Gwamnan ya fice daga Jam’iyyar LP zuwa APC, inda Jagoran Jam’iyar APC na Kasa Cif Bola Ahmed Tinubu ya karbe shi a wajen wani gagarumin biki da aka yi a Ibadan.