✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alaramman almajiran Arewatawa

Alaramman almajiran Arewatawa Mai gamba da gafakar girmamawa Tsangayar tsarin tsilla-tsilar tsayuwa Rumurmutsar romon ragon Romawa Tabahuwa ta hana almajirai karatun biyawa Da dankoko suke…

Alaramman almajiran Arewatawa

Mai gamba da gafakar girmamawa

Tsangayar tsarin tsilla-tsilar tsayuwa

Rumurmutsar romon ragon Romawa

Tabahuwa ta hana almajirai karatun biyawa

Da dankoko suke kewayawa

Suna neman abin cika kururu

Na-mujiyarsu yai kuru-kuru

Wai sun karanta babbaku da farfaru

kolo da titibiri na kaiwa da komowa

Inna uwata

Allazi Wahidin

Ni ne dan malam

Ki ba ni abin tauna

Uwardaki na samu gata

Ranar Juma’a

Nakan tuna A’ishatu fil jami’a

Mai kunna sham’a

Ta daga samma’a

kolo na walagigin turmutsitsin jama’a

Bobo da kwambo

Sai dan boko

kolo na laluben na-koko

Lalitar Alaramma ba  ko kwabo

Zamani ya shude

Wasunmu sun rude

Sun sanya almajirai sun baude

Su dai a ba su su dan tande

Hangen nesa ya turbude

Mai martaba da rawunna

Ka ga malumma da alluna

kolo ya karke da ganguna

Titibiri na ta laluben abin tauna

Ilimi an yanke masa kauna

Alifun ana Musulimun

Badatun agwagwa ke nan

Arnabun zomo na nan

Fa’un fa’un fatahat baban

Wato bude kofa ke nan

Alaramma mai imani

Ka dauki salon a zamani

Don dora almajirai a tafarkin sani

A inganta aikin iyaye da kakanni

Gardi da kolo su zam masana fanoni

Arewatawa a nai muku gani-gani

Ba kwa tafiya a turbar karni

Ku dai ku samu na cin makani

Ko kuna tuna umarni 

Ballantana munana ai musu hani

Alaramman almajiran Arewatawa, a irin wannan zamani matukar kana son daukaka kalmar Allah, kowa ya kara azama wajen bin umarni da hanin Mai-duka, Mai-kowa, Mai-komai, wajibi ne ka surka da tafiyar zamani, wadda ba ta baude daga kan turba ba. Saboda na fasko cewa gidan kowane Shehun shehinnai, matukar ya amsa suna ‘Shehu,’ ba “SHAHO’ ba, tabbas akwai gwanin BOBO DA kWAMBON BOKOKO a gidansa. Kuma akasari a jerin wadanda suka fasko jirgin tafiyar zamani ake samun ‘SHEHU MAGAJIN SHEHU,’ wanda hadafin manufarsa ba ta ta’allaka wajen tara taro da AHU, illa dai kawai al’umma ta yi SAHU-SAHU, don kada a maishe ta HUHUN MA’AHU.

Wata mahanga da na leko ita ce, ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA zai iya tarbiyyantar  da ALMAJIRAI su zama ATTAJIRAI, ko MALUMMAN MALAMMAI masu manufa TAKAMAIMAI. Tunda a wannan zamani masu aikata miyagun ta’adu, musamman samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya, sun kware a kutse da dandatsa a shafukan sadarwar na’ura mai kwakwalwa, kun ga ke nan ba a bukatar BADUHU layar zana. Sannan dan dambe da asakala in ya samu cikakken horon zilliya da iya kai naushi ba ya bukatar SAGAU da SHASHATAU. daukacin wadannan al’amura na nuni da cewa kULLE-kULLEN kULUMBOTO DA TSATSUBA DA TSUBBACE-TSUBBACE ba namu ba ne, ballantana har a kai ga TSATSUBAR TSUMBURBURAR TSATSUNBURUN, da ka iya haifar wa mutum mai imani wasan ’YAR BURUM-BURUM da imani, musamman kan al’amuran da suka shafi hani da umarnin Mai-duka.

Batu na ingarman karfen karafan titi taragon layi kwangiri, shirin raba kayan dundume kururu don WARWAREWAR ’YA’YAN HANJI da cikowar TUMBI, sai an yi wa kolo da Titibiri da Gardi babban tanadi. Sannan bayan Alaramma ya horar da su karatun Littafin Allah, wajibi ne a hada musu da ARJAMI, ko in ce a nusar da su  tsarin Ajami da Larabci, kamar yadda manyan shehunanmu irin su Na’ibi Sulaimanu Wali da Shaykh dahiru Maiga suka wallafa wagagen littatafai a wannan fanni.

Idan ma ba za a bai wa Alaramma lada da la’adar karatun babbaku da farfaru ba, to wajibi ne a samar masa garka da gayauna ya rika farda, rani da damina. Don ta haka ne kolo da Titibiri da ke hankoron kaiwa ga matsayinsa za su samu tudun dafawa na daga sana’ar abin dogaron gudanar da rayuwa.

’Yan makaranta masu koyon watsattsake da wangale shafukan mujallu da makalu a kasar Haurobiya kun san yadda ake dura wa Arewatawa ashariya ta uwa, ta uba wai sun ki kula da kolo da Titibiri har ma da gargadin garada. Wai kawai mun yasar da su suna ta walagigin da gararamba da dAN kOkON DABGEN dAN kANZO ko dUMAMEN dAN DAGO-DAGON dUNdUME-kURURU, yayin da na-mujiyarsu ya yi kURU-kURU, musamman a lokacin HUNTURU, a wani lokacin kuwa su yi ZURU-ZURU, domin ba su san yadda za su kulla ’yan DABARBARU ba.

A matsayina na babban Direban Alli a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintaciyar jaidar kasar Haurobiya, ina kira da kARAJIN MURYA ga iyayenmu masu martaba da rawuna da malumma masu alluna da su lalubo hanyar kyautata rayuwar kolo da Titiri, tun kafin su zama gargadin garada mai yawan gardama da rashin sanin makama. Ita Gwamnatin Baban-burin-huriyya akwai bukatar ta samar wa wadannan rukunin al’umma gine-gine na zamani, ta yadda za su samu natsuwa, ko sun daina tsuwwa, ballantana ta TABAHUWA ta daka musuTSAWA!