Aminiya

Albashi: Takaddama ta kaure tsakanin Gwamna Masari da malaman S. Power

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari

Takaddama ta kaure tsakanin Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina da malaman S. Power masu koyarwa a makarantun sakandaren da ke fadin jihar.

Malaman S. Power, wadanda suka shiga wani yajin aiki a yau Litinin bayan cikar wa’adin da suka bayar ya cika akan rashin biyansu albashin su har na tsawon watanni biyar.

A jawabin da ya yi, Gwamna Masari ya ce, a iya sanin sa wadannan malamai basu bin shi ko kwabo na albashin su domin duk wata sai yasa hannun amincewar a biya su hakkinsu. “Ko watan da ya wuce, Naira milyan 103 na bayar na albashin su ta ofishin jami’in da ke kula da wannan shiri”. Gwamnan sai ya zarge su da cewa, suna dai so ne su kawowa shirin sa na habaka ilimi a jahar tarnaki. “Saboda haka, tunda ba ma’aikata ba ne na din-dindin, in suka tafi yajin aikin sai mu biya su mu kuma kore su mu dauki wasu”.

Da suke mayar da martani akan wannan furuci na Gwamnan, kungiyar ta bakin Mataimakin Shugabanta na Jiha Kwamared Najeeb Mukhtar ya ce, “A iya sanin mu har zuwa wannan rana babu wanda ya biya ko kobo. Muna kuma kira ga shi Maigirma Gwamna da ya bincika domin sanin inda kudaden da yake biya suke shigewa. Kuma mu ba manufarmu ba ce ta kawowa kowane irin shiri na gwamnatinsa wani cikas ba ne. Mu da shi sai godiya da girmamawa. Mun dauki wannan mataki ne domin nuna bacin ran mu akan rashin sanin halin da muke ciki, bayan duk wata hanyar da ta kamata mun bita abin ya ci tura”.

Kamar yadda Aminiya ta jiyo daga wata majiya, shugabannin makarantun da wadannan malamai ke koyarwa a wajen su, basu ji dadin wannan mataki da wannan kungiya ta dauka ba. Sai dai sun yi fatan warware wannan matsala a cikin ruwan sanyi.

ADVERTISEMENT