✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alfanun da ke tattare da kiwon kifi – Raha

Shugaban kungiyar masu Kiwon Kifi na Najeriya, Alhaji Hussaini Raha ya bayyana cewa kiwon kifi na da riba  da kuma taimakawa wajen samar da abinci…

Shugaban kungiyar masu Kiwon Kifi na Najeriya, Alhaji Hussaini Raha ya bayyana cewa kiwon kifi na da riba  da kuma taimakawa wajen samar da abinci da  aikin yi ko sana’a ga al’umma.

Alhaji Hussaini wanda ya yi wannan bayanin a yayin tattaunawa da Wakilinmu,ya ce,  kiwon kifi dama yana da kyau idan kana yin kiwon kaji, sai ka hada da kiwon, saboda akwai tsarin da ake yi, a sanya sama kaji kasa kuma kifi, kashin da kajin suke yi yana fadawa ruwa zai zama abincin kifin ba sai ka ba su wani abinci daban ba. “Shi kiwon kifi madamar ka tanadi inda zaka tara ruwa, to ya fi kowane irin kiwo sauki, shi kansa ruwan da ake kiwon kifi da shi, idan ya koma tsanwa dinnan, wato gansakuka, to halittu ne dake samuwa wadanda kuma sukan zama abincin kifin, haka kuma idan ma an kwarfe yakan zama taki, wanda za’a rika zuba wa lambu inda zaka ga karas ko kabeji ya yi kyau sosai, ka ga idan kana kiwon kifi sai kuma gefe guda ka kafa lambu, ka ga ruwan da zaka rika ragewa na kifi shi zai zama na ban ruwa kuma ya zama taki ga lambun naka, kayan lambun naka kamar karas da kabeji ko tumaturi irin wanda ya rube ba zubarwa zaka yi ba, idan ka shanya ya bushe aka nika su garin yakan zama abincin dabbobi mai gina jiki sosai.”

Ya kuma kara da cewa, “Idan aka ce al’umma tana da abinci, to za ta magance kashi 85 cikin 100 na matsalolinta, ka ga lafiya ba ta samuwa sai da abinci mai kyau, idan mutane suka koshi suka samu lafiya matsalar asibiti za ta ragu za a samu sana’a babu zaman banza kuma yawan yin ta’addanci zai ragu a cikin al’umma,” in ji shi.