✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alfanun da ke tattare da noman bi-ni-da-zugu

Itacen Bini-da-zugu na daga cikin iatatuwan dake kunshe da alfanu masu yawan gaske kamar yadda masana ilmin kimiyya suka bayyana,  musamman bisa yadda al’ummar duniya…

Itacen Bini-da-zugu na daga cikin iatatuwan dake kunshe da alfanu masu yawan gaske kamar yadda masana ilmin kimiyya suka bayyana,  musamman bisa yadda al’ummar duniya ke karuwa kamar yadda bukatun bil-Adam ke karuwa a rayuwar yau da kullum. 

A yau babban abin da ya zama kalubale ga kasashen duniya shi ne karancin makamashi da kuma tsadarsa, tare da cewa amfani da man fetur da gas da kuma iskar gas ya na gurbata muhalli. A maimakon wadannan, masana sun gano amfanin mai da ake iya tatsarsa daga ‘ya’yan itace wadda ke dauke da sifofi irin na wadancan makamashi da muka ambata.

Wannan sanmfurin mai ana kiransa (Biodiesel) wato man da ake samu daga abubuwa masu rai. Tuni wasu kasashe su ka fara samar da makashin da ba na dangin man fetur ba. kasar Birazil ta dade tana sarrafa masara domin samar da makamashi. A kullum kasuwar makashin shuke-shuke ta duniya karuwa ta ke yi. 

Shuke-shuken da suke samar da man makamashi sun hada da wadanda ake ci kamar sukari da masara, da kuma wadanda ba a ci, kamar itacen Bini-da-zugu (Jatropha). Itacen Bini-da-zugu sananne ne a kusan dukan Nahiyar Afirka, inda ake yin shingayen kan iyakar gonaki da shi. Bini-da-zugu ba shi da tsawo yana manyan ganyaye, akasari ba ya wuce mita 3 zuwa 5, sai dai idan ya sami yanayi mai kyau ya kan kai mita 8 zuwa 10. Jikinsa sumul ya ke kuma idan an sare shi yakan fitar da ruwa mai danko. 

Ya na yin ‘ya’ya uku a cikin kwanso wanda idan ya bushe ya na saurin barewa. Yakan yi ‘ya’ya lokacin sanyi, amma idan kasa tana da laima sosai yanayi kuma na da kyau, itaciyar ta kan yi ‘ya’ya sau da dama a shekara. Bayan gano muhimmancin itacen Bini-da-zugu, kasashe da dama sun kafa cibiyoiyin bincike kan hanyoyin nomansa da sarrafa shi. 

A kasar Indiya da ta ke kan gaba wajen wannan hobbasa, an kafa wata cibiya ta yada noman Bini-da-zugu ta duniya (Centre for Jatropha Promotion). Ayyukan wannan cibiya sun hada da bincike kan yanayin halittar itacen da kuma hanyoyin nomanta da bunkasa ta da tatsar manta tare da sarrafa ta. 

Shuka Bini-da-zugu da sarrafa shi wata babbar hanya ce ta yaki da talauci, musamman ma a Nahiyar Afirka. Ana hasashen cewa sakamakon dumamar yanayi yawan amfanin gona a kasashen Afrika na kudu da Sahara zai ragu da kashi 20% nan da wasu shekaru kadan. Idan haka ya faru kasashen Afrika za su kara dogaro da kayan abinci masu tsada wadda za su shigo da shi daga kasashen waje. Haka kuma kimanin kashi biyu daga cikin uku na al’ummar kasashe masu tasowa su na samun kudaden shiga ne ta hanyar noma, saboda haka idan suka rungumi noman Bini-da-zugu za su sami karuwar arziki matuka.

kasashen su na iya samar da sababbin masa’antun sarrafa wannan itace, ayyukan za su karu, hanyoyin kasuwanci za su bude, sannan sababbin fasaha za su shigo. kasashe masu tasowa su na iya jan ragamar wannan harka ta samar da makamashi daga shuke-shuke, amma ba za su yi nasarar hakan ba sai sun wayar da kan manomansu.

Lallai ne sai manona sun fahimci wannan sabuwar hanya ta samar da makamashi, sai an ganar da su cewa shuka Bini-da-zugu zai kara musu abin hannu. Sai manoma sun tabbatar da cewa man wannan itace yana da kasuwa sosai kuma zai iya kawo sauyi a rayuwarsu, kana za su rungumi wannan aiki. A halin yanzu ana shuka itacen Bini-da-zugu domin samar da makamashi ko kuma gudanar da bincike a kansa a kasashe da dama, cikinsu akwai Indiya da Chana da Malesiya da Filifins da Kambodiya. A Nahiyar Afrika kuma akwai Mali da Ghana da Mauritania da Masar da Zimbabuwe da sauransu. 

Wasu cibiyoyin bincike sun bayyana cewa a wurin da kasa ta ke da kyau shuka itace 1,100 a kadada (hekta) daya zai ba da sakamako mai kyau amma idan kasar wuri ba ta da karfi sai a shuka kasa da haka. Ana samun kilogiram biyu a kowane itace, a wani yanayi kuma sama da haka. Ana samun ton 2.5 zuwa ton 5.5 a ko wani kadada, amma idan shukar ta kai shekara biyar masana sun ce abin da ake samu zai iya kaiwa ton 12. Man da ya ke cikin ‘ya’yan ya kai kashi 36 cikin 100, sannan a kasa mai matsakaiciyar kyau, ana iya samun ton 1.6 na mai a kadada guda. 

Bisa bayanan da wani shirin noma Bini-da-zugu a kasar Indiya ya bayar, ya nuna cewa shuka wannan itace zai samar da kudin shiga ga manoma, a shekarar farko za a sami kimanin dala 825 a kadada daya, sannan daga shekara ta biyar zuwa sama, kudin za su karu zuwa dala 4750. Dalilin hakan kuwa shi ne yayin da itacen ya kai matukar girmansa, ‘ya’yan da zai zuba duk shekara za su karu sosai. 

Koda yake wadannan alkaluma sun shafi yanayin wurin da ake wannan aiki a kasar Indiya ne, amma su na ba da kimanin abin za a samu a sauran kasashe. Bini-da-zugu ya na yi a wurare masu isashsen ruwan sama da wadanda su ke da karancinsa. Kamar sauran shuke-shuke, abubuwan da su ke tasiri a girmansa su ne yawan ruwa, taki, gyara da noma da sausu, duk da cewa ya na yi a wurare masu karancin ruwan sama da kasar da ba ta da karfi sosai. 

Wani abin sha’awa shi ne tunkuzar da za ta rage bayan an fitar da man Bini-da-zugu za a iya amfani da shi a matsayin takin da za a zuba wa gonar. Kowane shirin aikin gona, musamman ma wanda ya ke sabo, ya na bukatar tallafi daga gwamnati. Haka kuma akwai bukatar cibiyoyin binciken aikin gona su samar da cikakkun bayanai da hanyoyin noma itacen, da kuma ingantaccen irin da makamantarsu.

Gwamnatocin za su taimaka wajen hada kai da cibiyoyin bincike, wayar da kan jama’a, warware matsalar filayen noma, hada kai da masu sukuni domin kafa masana’antun tatsar man Bini-da-zugu da mai da shi tamkar man gas don yin daidai da bukatar motoci da injuna. Hakazalika hukumomi su na da rawar da za su taka wajen tallafawa kananan manoma da bashin kudi mai sauki, da sama mu su hanyoyin sayar da amfanin da za su samu da dai sauransu. 

Koda yake wasu masharhanta kan batun tabbatar da wadatar abinci sun yi tsokaci game da illar da noma shuke-shuke masu samar da makamashi za su yi wa aikin samar da abinci. Kuma tsoron da su ke ji na yin watsi da noman cimaka, abu ne da ya kamata a dube shi da kwau. Sai dai dangane da noman Bini-da-zugu ana iya cewa ba za a fuskanci wannan matsala ba saboda ba itace ne da ake ci ba, sabanin masara da rake da makamantansu wadanda ake nomawa a wasu kasashe domin a sarrafasu wajen samar da makamashi.

Har walau dai dole ne hukumomi su shirya wani tsari domin tabbatar da cewa noman Bini-da-zugu bai hana manona shuka kayan abinci ba. Wani abin da zai taimaka shi ne kebe wa wannan aiki wurare da su ke fako masu karancin ruwa, wadanda ba kasafai su ke jure wa noman cimaka ba, musamman ma yankunan da hamada ta ke neman kwacewa. 

A nan akwai riba biyu, ga amfanin da za a samu daga gonakin Bini-da-zugu ga kuma tare kwararowar hamada da kuma gyara kasa da tsai da zaizayewarta. Duk da cewa Bini-da-zugu ya na yi a wuraren da ba su da karfin kasa inda ba kasafai ake noman cimaka ba, amma akwai yiwuwar idan kwalliya ta biya kudin sabulu manoma su yi sako-sako na shuka kayayyakin abinci, saboda halin dan Adam na neman sauki.

Sai dai irin wannan sauki ya na iya zama sauri ne da zai haifi nawa ta bangaren kiyaye wadatar abinci. Saboda haka wani abin da ya kamata hukumomi su mai da hankali a kansa shi ne su kiyaye ta yadda noman makamashi ba zai raunana noman cimaka ba.