An nada Alhaji Umaru Nagwaggo a matsayin Babaselu na kasar Atowori wato kamar sarautar dan Madami a kasar Hausawa.
Sa’ilin da yake nada masa mukamin, Oba Olarewaju na Atowori ya ce akwai dimbin Hausawa da ’yan Arewa mazauna garin, amma irin rawar da Alhaji Umaru Nagwaggo ke takawa, ya ci a ba shi sarautar ma da ta fi ta Babaselu.
Oba Olarewaju ya yi fata sarautar ta kara wa Alhaji Umaru kwarin gwiwar ci gaba da ayyukasa na cigaban al’ummar Atowori, musammam na ganin yadda ake kara samun dankon zumunci tsakanin Hausawa da Yarbawa da ma sauran kabilun da ke zaune a tsakanin al’ummar.
Oba ya ce Alhaji Umaru ne ya kaddamar da taron lokaci-lokaci tsakanin masarautar da sauran jama’ar wannan wurin, ta yadda za a kankare kabilanci tsakanin mutanen da ke zaune a wurin, “Kuma tun daga lokacin muka yi ban kwana da duk wani abu da ake cewa tashin hankali ko kuma rashin fahintar juna”. Inji shi.
Da yake jawabinsa na godiyar ba shi wannan mukamin, Alhaji Umaru Nagwaggo ya ce wannan karramawar za ta kara masa kaimi wajen kara ayyukan cigaban al’ummar, saboda shi ma ya zama dan kasa, musamman ma da yake ya kwashe shekaru 24 yana zaune cikin wadannan mutanen.
Ya ce kuma tun daga wancan lokacin zuwa ranar da aka ba shi wannan sarautar zaune yake da daukacin jama’ar cikin lumana, musammam ma yanzu da harkokin tsaro, a wasu sassan Najeriya, musamman a Arewa, suka tabarbare. “Tun daga lokacin da na fara mu’amala da jama’ar da ke wannan wurin nake musu nasiha da su kankare kabilanci a zukatansu kuma su dauki juna ’yan uwa kuma hakan ya yi tasiri kwarai da gaske”. Inji shi.
Alhaji Umaru ya ce da a ce ’yan siyasa da ma shugabannin addini za su rika jaddada bayanan da ka kankare kabilanci a cikin al’umma, kana gwamnati ta rika daukar matakin ba-sani-ba-sabo ga duk wanda ya aikata ba daidai ba, to da an samu daidaituwar al’umma kuma batun jaddada kabilanci da rikicin addini da sun ragu ainun.
Alhaji Umaru Nagwaggo ya zama Baselu na Atowori
An nada Alhaji Umaru Nagwaggo a matsayin Babaselu na kasar Atowori wato kamar sarautar dan Madami a kasar Hausawa. Sa’ilin da yake nada masa mukamin, …