✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alhazan Kaduna 546 sun dawo gida Najeriya

A yau juma’a ne Jirgin da ke dauke da alhazan jihar Kaduna su dari 546 ya iso gida Najeriya daga kasar Saudiya inda suka gudanar…

A yau juma’a ne Jirgin da ke dauke da alhazan jihar Kaduna su dari 546 ya iso gida Najeriya daga kasar Saudiya inda suka gudanar da aikin Hajjin bana.

A cikin wata Sanarwa dauke da sa hannun kakakin Hukumar jindadin Alhazai ta jihar Kaduna, Yunusa Abdullahi ya ce Jirgin ya iso filin Jirgin sama ne a jihar Kaduna da misali karfe 11:30 na safe.

Jirgin Max ne ya dawo da alhazan kuma sun dawo ne tare da jakunkunansu.
Dawowarsu alama ce ta fara jigilar Alhazan jihar Kaduna Daga kasar Saudiya.

Akalla Alhazai 3,546 ne suka gudanar da Aikin Hajji daga jihar Kaduna a bana.