✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ali Nuhu ya samu magoya miliyan daya a Instagram

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu a yanzu ya tara mabiya miliyan daya a shafinsa na sada zumunta na Instagram. Ali Nuhu wanda a ranar…

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu a yanzu ya tara mabiya miliyan daya a shafinsa na sada zumunta na Instagram.

Ali Nuhu wanda a ranar Juma’ar da ta gabata ya yi bikin cika shekara 45 ya samu mabiyan ne bayan ya fitar da sakonni da hotuna da bidiyo da yawansu ya kai dubu 6 da 303 a shafin na Instagram.

Jarumin wanda shi ne Manajan Daraktan Kamfanin Shirya Fina-Finai na FKD Productions shi ne jarumi na uku a Kannywood da yake da mabiya miliyan daya a Instagram bayan jaruma Rahama Sadau da kuma Hadiza Gabon.

Aminiya ta gano cewa jarumin wanda yake bin mutum 3,062 a shafin Instagram ya gode wa mabiyansa a shafin na Instagram a ranar Juma’ar da ta gabata.

Ya ce, “Ina godiya ga mabiyana har zuwa wannan kadami, na gode wa wadanda suka yi bikin zagayowar ranar haihuwata, na gode wa wadanda suka zo muka kalli fim din ‘Hafeez da su, sannan na gode wa wadanda suka shirya wasan kwallon kafa don murnar zagoyawar ranar haihuwata.”