✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aliyu Gusau ne Ministan Tsaro

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya nada sababbin ministoci 11 da suka haɗa da Janar Aliyu Mohammed Gusau mai ritaya daga Jihar Zamfara a matsayin…

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya nada sababbin ministoci 11 da suka haɗa da Janar Aliyu Mohammed Gusau mai ritaya daga Jihar Zamfara a matsayin Ministan Tsaro.
Sauran ministocin da Shugaba Jonathan ya nada kuma ya rantsar a shekaranjiya Laraba su ne Alhaji Aminu Wali daga Jihar Kano a matsayin sabon Ministan Hulda da kasashen Waje, sai Misis Lawrencia Laraba Mallam daga Jihar Kaduna Ministar Kula da Muhalli. Mista Boni Haruna daga Jihar Adamawa shi ne Ministan Kula da Matasa, yayin da Hajiya Asabe Asama’u Ahmed daga Jihar Neja ta zama Ministar Aikin Gona, Misis Akon Eyakenyi ita ce Minista a Ma’aikatar kasa da Muhalli, sai kuma Abduljelili Adesiyan Ministan Harkokin ’Yan sanda.
Sauran ministocin sun hada da Musiliu Obanikoro daga Jihar Legas Minista a Ma’aikatar Tsaro, sai Muhammed Wakil daga Jihar Borno Minista a Ma’aikatar Makamashi, yayin da Alhaji Khaliru Alhassan daga Jihar Sakkwato ya zama Minista a Ma’aikatar Lafiya.
A shekaranjiyar Shugaba Jonathan ya cire Ministan Wasanni, Malam Bolaji Abdullahi, inda nan take ya maye gurbinsa da Tamuno Danagogo.
Yanzu dai hankali zai fi karkata ne ga Ministan Tsaro Janar Aliyu Gusau sakamakon irin kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin Arewa maso Gabas, inda a cikin wannan watan kadai anka kashe fiye da mutum 300.