Daily Trust Aminiya - Aliyu Yakubu Lame: Yadda dan jarida ya zama Sarkin Yakin Bau
Subscribe

Aliyu Yakubu Lame: Yadda dan jarida ya zama Sarkin Yakin Bauchi

Alhaji Aliyu Yakubu Lame, yana daya daga cikin mutum hudu da Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaimanu Adamu ya nada a sarauta, inda aka nada shi a  Sarkin Yakin Bauchi. Sarkin Yaki babbar sarauta ce a Masarautar Bauchi ita ce ta uku Bayan Galadima da Madaki, wanda kuma daya ne daga cikin masu Zaben Sarki. Aminiya ta zanta da sabon Sarkin Yakin kamar haka:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Aliyu Yakubu Lame dan marigayi Sarkin Yakin Bauchi Alhaji Yakubu lame jikan Abubakar jikan Barayan Darazau Alhaji Sulaiman. An haife ni ranar 19 ga Mayun 1969 a  Unguwar Lamsula a Maiduguri, lokacin mahaifinmu yana kwamishina. Bayan an ba Bauchi jiha sai muka dawo Bauchi aka sani a firamaren Bakaro na yi shekara 6 daga nan sai karatu ya kai ni Kwalejin Horar da Malamai (TC) da ke Kangare, kafin ta zama ‘Unity College’. Daga nan sai  aka kai ni Duguri, sai mai gidanmu ya ce yana bukatata in zauna a nan, sai ya zo ya samu shugaban makarantarmu aka kai ni Gumau, wato kasata ke nan, a nan na zauna na shekara biyar bayan na na gama sakandare sai na tafi Kwalejin Sana’a da Kere-Kere ta Jihar Bauchi (BACAS).

Ina da mata uku da ’ya ’ya 17 maza goma 11 mata shida, muna rokon Allah Ya yi wa zuriyarmu da al’ummarmu albarka Ya jikan iyayenmu da magabatanmu, muna kuma dada horon jama’a a zauna lafiya da juna.Burinmu a zauna lafiya domin samun ci gaban kasa.

Yaya gwagwarmayar aiki?

Bayan na gama BACAS, sai na samu aikin Kwastam zamu tafi a tasiye mai gidanmu ya ce in yi hakuri in zauna. Na yi hakuri har wata uku sai na je na same shi na ce masa zama ya dame ni. Lokacin akwai dan uwana Dokta Ibrahim Yakubu Lame (Allah Ya jikansa) yana Kwamishinan Watsa Labarai da Al’adu na Jihar Bauchi, sai ya yi masa magana aka dauke ni a ma’aikatar na samu kaina a Majalisar Jiha. Na samu kaina cikin aiki tun ina da shekara 18 a can na yi kwasa- kwasai har na zama kwararren mai daukar hoto na karanta cinematograph, na yi kwas din shirya fina-finai da na aikin jarida.

Lokacin da na fara koyon rubuta labarai muna tare da Jihar Gombe shi ne suka tura ni na je na yi kwas din aikin jarida. Da na gama sai na zo ina aiki da sashin siyasa a Gidan Talabijin na Jihar Bauchi (BATB). Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Gombe, sai aka dawo da ni sashin kasuwanci na je na yi Babbar Diploma kan kasuwanci a Sashin Harkokin Kasuwanci na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU). Daga baya na fara karatun digiri sai na samu hadari na karye, karatun bai yiwu ba sai na tsaya. Daga nan na ci gaba da aiki har na rike mukamin Darakta kafin in bar aiki.

Alhamdulillahi ni da abokan aikina mun zauna kamar dangi shekarata 32 ina aiki da su amma babu wanda zai ce mun yi sa-in-sa da shi ko mun bata, ko wani abu na rashin fahimta. Na ji dadin zama da su su ma sun ji dadin zama da ni.

Yaya ka ji lokacin da aka nada ka Sarkin Yakin Bauchi?

Godiya ta tabbata ga Allah,  gaskiya na ji dadi kuma na yi farin cikin da ban taba irinsa a rayuwata ba. Saboda burin kowane dan gidan sarauta ya gaji mahaifinsa. A wannan rana ba ni da kalmar da zan fada wadda za ta bayyana irin farin cikin da nake ciki, da kuma dadin da nake ji a raina da samun natsuwa da kwanciyar hankali. Ka san yanayin neman sarauta akwai gwagwarmaya tunda aka fara gwagwarmayar nan ba barci, tunanin shiga can fita can. Da ma rubutacce ne duk abin da ya same ka Allah Ya riga Ya shirya shi, haka abin da ka rasa Allah Ya shirya haka.Farin cikina Ubangiji Ya cika min burina na gode wa Allah, kuma na gode wa Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulkadir Kauran Bauchi kuma na gode wa Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu da ’yan majalisarsa.

Sarautar Sarkin Yaki babbar  sarauta ce a Bauchi mene ne aikin Sarkin Yaki?

Daga jin sunan ka san inda aka nufa, domin shi kansa Mai martaba Sarkin Bauchi, Sarkin Yaki ne a fadar Sarkin Musulmi. Shi kuma Sarkin Bauchi Sarkin Yakinsa ne. Iyayenmu su suka jaddada Musulunci a kasar nan, sarauta ce mai daraja da dimbin tarihi sarauta ce da ta yi aiki wajen tabbatar da addini da gaskiya da adalci kuma sarauta ce wacce a  dalilinta aka zauna lafiya. Dalilin iyaye da kakanninmu aka kyautata rayuwar al’umma a yau har wadansu suka bar saka ganye suka dawo saka sutura. Dukkan wadannan ayyuka na alheri kakanninmu sun yi su ne ba don komai ba sai don kwadayin samun lada a wajen Allah Madaukakin Sarki. Kuma muna rokon Allah Ya jikansu Ya karbi ayyukansu kamar yadda Ya yi alkawari cewa duk wanda ya shiryar kan aikin alheri, Allah Zai ba shi lada kamar na wanda ya shiryar din. Muna rokon Allah Ya bai wa kakannin namu lada cikin ayyukan alheri da suka shiryar.

Allah Ya cika maka buri wadanne ayyuka za ka gudanar?

Duk abin da zan yi, zan gudanar  da shi ne a kan abin da magabata suka yi, wato jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da adalci da gudanar da ayyukan alheri ga al’umma. Sai dai abin da nake roko fata nagari da addu’o’in Allah Ya taimake ni, saboda komai yana zuwa da zamani komai dama ce Allah Yake ba ka. Tunda ga wannan dama ta samu zan yi cikakkiyar biyayya ga Mai martaba Sarkin Bauchi da sauran ’yan majalisarsa da ’yan uwana, za su san cewa suna da da, haziki jarumi jajirtacce mai kishin al’umma mai kishin sarauta, saboda ba na shakka in dai a kan harkar da ta haife ni ne zan rike hannu biyu zan kare hakkin al’umma kuma zan tsare mutuncin masarauta da mutuncin Sarki. Duk inda nake ba zan yarda wani abu sabanin haka ya faru ba, kuma zan tsaya abin da duk al’umma ba ta so ba zan yi ba, abin da suka rasa in dai idona ya gani ko kunne na ya ji zan tsaya in yi iya kokarina a samar da shi.

Mene ne babban aikin Sarkin Yaki a fadar Sarkin Bauchi?

Wato a baya duk lokacin da aka zo maganar farmaki lokacin jihadi Sarkin Yaki shi ne a gaba, kuma duk masu nada  sarauta kowa akwai inda ya tsare. Amma idan Sarkin Yaki bai fito ba, hankalin Sarki ba ya kwanciya. Saboda shi ne kwamandan yakin ka tafi yaki ba wanda zai shirya maka kuma da izinin Allah duk ranar da yake gaba a kan samu nasara. Shi ne ya ba mu dama muka samu gurbinmu mai karfi kuma shi ne ya ba mu dama ake ba mu girma a fadar Mai martaba Sarkin Bauchi.

Amma aikin da yake yi a yanzu da zamani ya canja komai ya dawo irin na Bature, aiki muke yi irin na ofis a fada domin kyautata rayuwar al’umma, kuma mukan bai wa Mai martaba shawara kan al’amuran yau da kullum, yadda muka samu kanmu cikn manyan hakimai, Galadiman Bauchi shi ne a gabanmu, sai Madakin Bauchi sai Sarkin Yakin Bauchi.

A cikin wannan tafiya lokacin da marigayi mai  gidanmu shi ya jagoranci gidan nan shi yake jagoranci a fadar Mai martaba yanzu ga tafiya ta taho kuma ina fata yadda mahaifina ya rike wannan, ya kuma tafiyar da dukkan al’amuran ofis har masarautar Bauchi ta yi fice to idan na samu dama zan gudanar da aikin ofis din nan yadda ya kamata. Tunda yanzu ba yakin ake yi ba ballantana a ce zan jagoranci runduna a bayana, yanzu aikin ofis ne na wanzar da alheri da ba kowa hakkinsa.

Matsalar tsaro tana cikin matsalolin da masarautu ke fama da su, kuma yankinka na kasar Lame yana dauke da dazuzzuka da ke zama mafaka ga miyagu wane mataki za ka dauka don kawo zaman lafiya a yankin?

Wane mataki na fara dauka dai? Sanin haka daga nada ni na je na zauna da dukkan  dagatai kuma na fada musu da dan gari akan ci gari, don haka duk abin da ya fito ko baki suka zo mu sani. Wannan shi ne zai ba mu dama mu dakile abin kafin ya addabi mutanen gari.

Sannan  na yi zama da kungiyoyin Fulani na gargade su na kuma ja kunnensu na yi musu nasiha. Na ce abin kunya ne abin bakin ciki ne duk wani mummunan abu idan ya fito za a ce Bafullatani ne, wanda a baya ba haka abin yake ba. Don haka su je su zauna a tsakaninsu kowa ya san abin da ya yi Ranar Lahira zai je ya tarar, kuma su yi magana da al’ummarsu su nuna musu illar fitina da rasa rayuka. Domin cikin abin da Allah Ya halitta babu abin da darajarsa ta kai ta dan Adam. Don haka mu zauna lafiya da juna.

Alhamdulillahi duk wanda na yi zama da su da malaman kungiyoyi na ce su je su yi ta yi mana addu’ar zaman lafiya mu da shugabanninmu. Kuma mun dawo mun yi zama a kan tarbiyyar yara yadda za a yi mu dakile shan miyagun kwayoyi da sauran kayan maye da munanan dab’iu da yara ke yi wanda rashin aiki ke sa su. Kwanan nan zan je in sake zama da dukkan masu ruwa-da-tsaki na Gwamnatin Tarayya da jiha da kananan hukumomi, mu zauna mu nema wa yaran nan makarantu mu nema musu aikin yi wanda ya faskara kuma sai mu kai shi inda za a hukunta shi.

texem
More Stories